Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ina Kallo Ƙanina Sani Ya Rasu Ba Yadda Na Iya- Ɗangote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya bayyana yadda ƙaninsa, Sani Ɗangote ya rasu a gabansa. A ranar Lahadin da ...Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya bayyana yadda ƙaninsa, Sani Ɗangote ya rasu a gabansa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Sani Ɗangote, wanda shi ne Mataimakin Rukunin Kamfanoni Ɗangote, ya rasu a wani asibiti da ke Miami a Amurka.

Yayin da ya tarbi Jagoran Jam'iyya mai Mulki, APC, Bola Tinubu a gidansa da ke Kano a ranar Juma'a, Ɗangote ya bayyana cewa a gabansa da maihaifiyarsu, da ƴaƴan Sani Allah Yai masa cikawa.

Ɗangote ya ƙara da cewa, da su ka je asibitin, a lokacin da a ke duba Marigayin, likitocin sun faɗa musu cewa nan da awa ɗaya zai rasu.

Ya ƙara da cewa lokacin da Marigayin ya ke kwance an jona masa na'ura,  "abin baƙin ciki da ciwo shi ne cewa mu na kallo  ta na'ura har ya rasu. Wannan abu da tashin hankali ya ke.

"Amma haka Allah ya tsara. Kuma kowa zai rasu. Ba wanda ya san wanene gawar fari. Ko mai kuɗi ko talaka. A matsayin mu na musulmai, mun yi imani da mutuwa.

"Mu na roƙon Allah da ya jiƙansa da gafara.

"Mai girma Gwamna, mu na godiya da wannan karamci da ka ke mana. Mun gode sosai, Allah ya saka da alheri,"

A na shi jawabin, Tinubu ya bayyana cewa kuɗi ba zai iya siya rayuwa ba, inda ya ce idan mutuwa ta zo ba abin da a ka isa a yi.

Ya yi kira ga Dangote da sauran dangin Marigayin da su dage da yi masa addu'a, in da ya ce ya zo Kano me domin yin ta'aziyyar mamacin.

No comments