Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jaafar Jaafar Ya Sadaukar Da Naira Miliyan Daya Ga Marasa Lafiya

Mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar ya bayyana cewa zai bai wa shirin IN DA RANKA na gidan Rediyon Freedom Kano sad...


Mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar ya bayyana cewa zai bai wa shirin IN DA RANKA na gidan Rediyon Freedom Kano sadakar tarar Naira dubu dari takwas (N800, 000) É—in da kotu ta ci gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje wanda kuma gwamnan ya biya shi saboda bata masa lokaci da ya yi a shari'a. 

Ganduje dai ya kai ƙarar Jaafar babbar kotu da ke Kano ne a 2018 bisa laifin ɓace da ƙage bayan da fitaccen ɗan jaridan ya wallafa wasu faya-fayan bidiyo da su ka nuna gwamnan ya na amsar dalolin Amurka a matsayin na goro.

To amma daga bisani, sai kotun ta yi  umarnin Ganduje da  ya biya Jaafar É—in Naira 800,000 domin É“ata masa lokaci bayan da gwamnan ya janye Æ™arar.

A wata hira da Jaafar ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano a ranar Asabar, Jaafar ya bayyana cewa zai bayar da gaba ɗaya kuɗin ga shirin IN DA RAN KA da ke ɗauke da wani ɓangare na neman taimakon lafiya da kuɗin makaranta a gidan rediyon.

Jaafar ya ƙara da cewa zai cika Naira 200,000 (dubu dari biyu) a kan kuɗin su zama Naira 1,000,000 (miliyan daya) domin a taimakawa masu ƙaramin ƙarfi.

A yanzu haka Jaafar ya samu mafaka a ƙasar Ingila bayan da ya yi ƙorafin cewa a na barazana ga rayuwarsa sakamakon fallasa faya-fayan dalar da ya yi.

No comments