Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Jami'ar MAAUN Ta Taya Dr. Fanda Murnar Naɗa Shi Mukamin Mataimakin Darakta A Makarantar Horas Da Dabarun Kiwon Kifi

Hukumar gudanarwar ta Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), ta taya Dakta Aminu Wada Fanda murnar nadin...



Hukumar gudanarwar ta Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), ta taya Dakta Aminu Wada Fanda murnar nadin da aka yi masa a matsayin Mataimakin Darakta a Makarantar koyar da dabarun kiwon kifi na Bagauda da Magaga.

Kafin nadin na shi, Dakta Fanda ya kasance memba a Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano dake Wudil.

Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun wanda ya kafa kuma shugaban Jami'ar MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Laraba.

Ya bayyana nadin Dr. Fanda a matsayin wanda ya cancanta bisa la’akari da irin dimbin gogewar da yake da shi a fannin karatu da aiki.

Farfesa Gwarzo ya bayyana fatansa na cewa sabon mataimakin Daraktan zai yi amfani da kwarewarsa wajen tallafa wa Hukumar gudanarwar makarantar domin ciyar da ita gaba.

"A don haka, a madadin kaina da kuma Hukumar gudanarwar MAAUN, ina taya ku murna bisa nadin da aka yi ma ku a matsayin Mataimakin Darakta a Makarantar kiwon kifi na Bagauda da Magaga,” in ji Farfesa Gwarzo.

Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya yi masa jagora ya kuma kare shi a yayin da yake sauke sabon nauyin da aka dora masa.

No comments