Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JIBWIS ta Koyawa Mutane 300 Sana'o'in Dogaro Da Kai A Garin Bauchi

Daga Sumayya Idris A ranekun 6/7/10/2021 ne kungiyar jama'atu izalatil bid'a wa'kamatis sunnah ta tarayyar Nijeriya ...


Daga Sumayya Idris

A ranekun 6/7/10/2021 ne kungiyar jama'atu izalatil bid'a wa'kamatis sunnah ta tarayyar Nijeriya karkashin jagorancin shugaba Abdullahi Bala Lau da Daraktan sashen koyar da sana'oin dogaro da kai, Sheikh Injiniya Aliyu Burga Azare ta koyawa mata da maza sama da 300 sana'o'i mabambamta domin dogaro da kai.

Haka zalika kungiyar ta bayar da tallafi ga wasu daga cikin mahalarta taron domin karfafa su.

Wakiliyarmu ta labarto cewa; bayan an koyar da sana'o'i iri daban daban ga mata da maza tare da gabatar da laccoci akan abin da aka koya musu da muhimmancinsa ga al'ummar musulmi ne sai Injiniya Burga ya yi jawabi mai tsawon gaske dake nuni da godiya Allah da yasa aka sami dukkan nasarorin da ake nema gami da godiya ga shugabanin musamman gwamnan jihar Bauchi da sauran manyan baki da suka taso daga nesa "suka halarci wannan taro mai muhimmanci da muka gabatar wanda suka bayar da gudummawarsu na abubuwa da dama domi ganin taron ya tabbata", inji shi.

Kuma ya jinjinawa mutane kamar su Sanata Gumau.

Shima shugaban kungiyar na kasa Sheikh Bala Lau ya mika godiyarsa ga shugaban wannan sashi bisa yadda ya jajirce har aka sami nasarar gudanar da taron kuma ya yi kira da 'yan baya da su yi koyi da irin wannan himma tasa tare da yi masa fatan alheri da duk jama'ar dake aiki a karkashinsa.

Wannan taro an gudanar da shi ne a babban dakin taro na tunawa da Shiek Jafar Adam dake jihar Bauchi.

No comments