Kabir Kofa Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ya Rasu



Mun samu labarin rasuwar Honorabul Kabir Ahmed Kofa tsohon Kakakin Majalissar dokokin jihar Katsina bayan fama da rashin lafiya kamar yadda Katsina Post ta labarto. 

Wata majiya ta shaidawa jaridar Katsina Post cewa ya rasu jiya da dare a wata asibiti dake a cikin birnin Katsina.

Ya shaida cewa za a gabatar da sallar jana'izarsa da misalin karfe goma na safiyar yau a masallacin GRA Katsina.

Post a Comment

0 Comments