Daga Muhammad Farouk Kafar watsa labarai ta MADOGARA TV/RADIO mai shafin Intanet a www.madogara.com.ng ta nada Ammar Muhammad ...
Daga Muhammad Farouk
Kafar watsa labarai ta MADOGARA TV/RADIO mai shafin Intanet a www.madogara.com.ng ta nada Ammar Muhammad Rajab a matsayin Editan kafar. Aikin na shi a hukumance ya fara ne daga watan Nuwamban shekarar da muke ciki.
Nadin
dan jaridar a matsayin Edita ya biyo bayan sabbin gyare-gyaren da kafar ta
dauko domin inganta aikinta a fagen watsa labarai na zamani.
Bayan
tabbatar da shi a matsayin Edita, Ammar Muhammad Rajab ya wallafa a shafinsa na
Facebook cewa; “a hukumance na fara aiki da kafar watsa labaran zamani ta
MADOGARA ( www.madogara.com.ng ) Zan yi
aiki da kafar a matsayin Edita”.
“Ayyukana
shi ne rubuta labari, tsarawa da kuma kula da hanyoyin isar da su, tare da jagorantar marubuta, masu fassara, Æ´an
jaridar zamani, masu tace rubutu, da masu zanen hoto, sanya idanu kan ayyuka
daban-daban da aka yi, tare da kuma gyara rubutu domin tabbatar da ya bi ka'ida
da salo bisa doron ka'idodin aikin jarida”, ya lurantar.
“Kafar
watsa labaran na da sashen Turanci da Hausa, zan yi aiki a sashen Hausa. Insha
Allah a shirye nake na fuskanci wannan sabon kulen aikin jarida na zamani”, ya
jaddada.
Ammar
Muhammad Rajab ya kwashe akalla
shekaru 10 yana aikin Jarida. Ya fara aikin jarida ne da jaridar ALMIZAN.
Sannan ya yi aiki da kafafen watsa labaran na cikin gida da na waje da suka
hada; LEADERSHIP A YAU (Abuja), Dimokuradiyya (Kaduna), Tarayya
(Kaduna), Tamola (Kaduna), THE MAIL ONLINE PUBLISHERS LTD (Abuja),
Almahdi TV (Pakistan), MADUBI (Abuja), NaijaFox (Iran), Nigeria21
(Iran), EDUCATION MONITOR LTD (Abuja/Keffi).
MADOGARA kafar watsa labarai ce da wasu zakakuran ‘yan jarida suka bude a
matsayin mai zaman kanta wacce za ta rika yada labarai da rahotanni na gaskiya
da kuma muhimman bayanai. Kafar na watsa ayyukanta bisa tsare-tsare da dokoki
irin na aikin jarida.
Za
ku iya bibiyar kafar watsa labaran a wadannan shafuka kamar haka;
Facebook:
Madogara TV/Radio
Twitter:
@Madogaratv
Website:
www.madogara.com.ng
WhatsApp:
09121740284
No comments