Kotu a Koriya ta arewa ta yankewa wani matashin daurin rai da rai, sakamakon Kallon shirin SQUID GAME (Film din da kamfanin Netf...
Kotu a Koriya ta arewa ta yankewa wani matashin daurin rai da rai, sakamakon Kallon shirin SQUID GAME (Film din da kamfanin Netflix ke haskawa).
An yanke masa hukuncin tare da wasu abokansa biyar bayan da suka kalli fim din tare.
Cikin abokan ko wannen su zai kwashe shekaru biyar a gidan yari kamar yadda Jaridar Daily Mail ta labarto.
A cikin dokokin kasar ta Koriya ta Arewa ta haramta shigo da dukkanin wani abu ciki harda Fim daga kasashe yamma da kasar Koriya ta Kudu cikin kasar ta. A karkashin dokar idan aka kama mutum da shigowa ko kallo ko rabawa, za a yanke masa hukuncin kisa.
A cewar rahoton Daily Mail da yiwuwar a kashe wanda ya shigo da Fim din ta hanyar harbi. Sai dai rahoton ya ce a wani hukunci da aka yanke, dalibin da ya shigo da Fim din daga Chana an yi masa daurin rai da rai a gidan yari, a yayin da sauran daliban da suka kalli Fim din a tare za su shafe shekaru biyar-biyar a gidan yari.
No comments