Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kallo.ng: An Samar Da Sabuwar Manhajar Yaɗa Al'adun Hausa

Mu na farin cikin sanar da ku manhajar nishaɗantarwa ta yanar gizo mai suna kallo. An ƙirƙiri kallo.ng ne domin sada masoya nish...Mu na farin cikin sanar da ku manhajar nishaɗantarwa ta yanar gizo mai suna kallo.

An ƙirƙiri kallo.ng ne domin sada masoya nishaɗi, musamman ma masoya fina-finan Hausa daga wayoyinsu na hannu ko kwamfutarsu a gida ko a wajen sana’o’insu.

Manhajar Kallo.ng za ta kawo muku daɗaɗan shirye-shirye da sabbin fina-finai, fina-finai masu dogon zango, shirye-shirye na musamman da kuma kaɗe-kaɗe iri daban-daban.

Za ku iya shan kallo shirye-shiryenmu ta adreshin mu na yanar gizo, ko ku sauke manhajar kallo a na'ura mai ƙwaƙwalwa, wayoyin andiroyid ko kuma iOS wanda zai zo muku nan ba da daɗewa ba.

Burin mu shine mu nishaɗantar da ƴan Afrika a cikin nahiyar da kuma waɗan da ke zaune a ƙasashen waje ta hanyar kawo muku kayatattun shirye-shirye domin ci gaban al'adu da mu'amular mu, ta yadda za mu matso da ƴan Afrika kusa da gida ko a ina su ke a faɗin duniya ta amfani da manhajar mu da bata katsewa.

Tabbas muna sane da irin rawar da fina-finan Hausa ke takawa wajen haɗa kan al'umma ta hanyar sadar da masu kallo daga gurare daban-daban domin ilimantarwa da kuma saka ko kuma kawo canji ga masu kallo da  hada kan al'umma domin kawo ci gaban al’adunmu.

Ko shakka babu Kannywood ita ce uwa-ma-bada-mama a harkar shirya fina-finan Hausa. Da haka ne za mu haɗa hannu dasu domin kawo canji mai kyau ta hanyar haɗin gwiwa da karbar changin da zamani ya kawo. 

Wannan ne ya sanya kuna zaune a gidajen ku za mu riƙa kawo muku dina-finai na da waɗan da su ka yi tashe a shekarun da su ka gabata, da kuma na zamani.

Babu tantama cewa an san hausawa da son nishaɗi, to ga kallo.ng za ta share muku hawayen ku.

Kallo.ng na ƙarƙashin Spacekraft Media Limited, kamfani ne na gida wanda ya ke mallakar wasu yan kasa masu  ra'ayin ci gaban al'adunsu.

No comments