Daga Umar Shuaibu Kamar yadda kafar watsa labarai ta Tasnim dake ƙasar Iran ta wallafa, Fatemeh Norouzi mai shekaru 122 dake ray...
Daga Umar Shuaibu
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Tasnim dake ƙasar Iran ta wallafa, Fatemeh Norouzi mai shekaru 122 dake rayuwa a garin Tobat-e Jam ke riƙe da kambun wanda yafi kowa tsufa a wannan duniyar a halin yanzu.
Kean Tanaka mai shekaru 118 daga ƙasar Japan da kuma Jean Kalman mai shekaru 122 da kwana 164 daga ƙasar Faransa wanda ya rasu a shekarar 1997 suna cikin wanda suka riga Fatemeh Norouzi riƙe wannan mukamin.
A yanzu dai tana da shekaru 122 da watanni 2 da kuma kwana 4.
A yayin hira da kafar watsa labarai ta Tasnim, Fatemeh ta bayyana cewa, tun tana da shekaru 25 a Duniya aka mata aure kuma ta iya karatu da rubutu.
Da wannan shekarun na ta, Fatemeh na iya tashi ta je ta yi alwala tare da taimakon Sanda, tana kuma iya yin Sallah sau 5 a kowacce rana. Sai dai tana fama da ciwon zuciya da hawan jini, kuma tana da rauni wurin ji da gani.
No comments