Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kamfanin Dangote Ya Sanar Da Rasuwar Mataimakin Shugaban Sa Sani Dangote

Kamfanin hamshakin Attajirin Afirka Aliko Dangote ya sanar da rasuwar mataimakin shugaban rukunoninsa Alhaji Sani Dangote. Dango...


Kamfanin hamshakin Attajirin Afirka Aliko Dangote ya sanar da rasuwar mataimakin shugaban rukunoninsa Alhaji Sani Dangote.

Dangote ya rasu ne a kasar Amurka ranar Lahadi sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da ita, kuma tuni jama’a suka fara aikewa da sakon ta’aziya ga ‘yan'uwa da iyalansa.

Sani Dangote ya yi fice a bangaren aikin noma da harkokin man fetur da kuma bankuna, yayin da yake rike da mukaman shugabancin kamfanoni da dama dake karkashin rukunin kamfanin Dangote.

Mataimakin shugaban rukunin kamfanin Dangoten yayi kuma fice a bangaren wasan polo, abin da ya bashi damar zama shugaban kungiyar polo ta Nijeriya da kuma ziyarar kasashe da dama wajen yin wasan cikin su harda Ingila da Argentina.

Daga cikin wadanda suka fara aikewa da sakon ta’azziyar su harda tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar wanda ya bayyana shi a matsayin hamshakin ‘dan kasuwar da ya taimaka da dama wajen ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.

No comments