Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kamfanin Shirya Finafinai ‘UK Entertainment’ Ya Maka Hafsat Idris A Kotu

Premium Times ya labarto cewa; wani kamfanin shirya fina-finai, mai suna ‘UK Entertainment’, ya maka fitacciyar jarumar Kannywo...


Premium Times ya labarto cewa; wani kamfanin shirya fina-finai, mai suna ‘UK Entertainment’, ya maka fitacciyar jarumar Kannywood, Hafsat Idris a Kotu, bisa zargin karya alkawarin wata kwangila da ta saka wa hannu tsakaninta da kamfanin.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan ƙara wanda aka shigar a gaban wata babbar kotun Kano mai lamba 14 a karamar hukumar Ungogo, an zargi jaruma Hafsat Idris da karbar Naira miliyan 1.3 domin ta fito a wani shirin talbijin amma ta kauce bayan ta cake kuɗin a aljihun ta ki cika alkawarin da ta ɗauka na amince wa wannan yarjejeniyar da dukan su bangarorin biyu suka sanya wa hannu.

Kamfanin ya bukaci Hafsat ta biya shi Naira miliyan 10, kuɗin hasarar da ya yi wajen shirya ƙayan da za a yi amfani da su jarumar ta ki bayyana a lokacin daukar wannan shiri.

Kamfanin ya roki kotu ta tilasta wa jarumar ta biya waɗannan kuɗaɗe.

Sai dai kuma Hafsat da ake tuhuma ta hannun lauyanta, ta maida martani kan ikirarin da zargi da wannan kafani ya yi a kanta.

Alkalin kotun ya ɗage Shari’a zuwa wani lokaci.

No comments