Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Karawa Sarakuna Karfi Zai Taimakawa Harkar Tsaro, Inji Marafan Jere Abubakar Tambuwal

      Marafan Jere kuma Dallatun Tafa Alhaji Abubakar Tambuwal. Daga Fatima Idris Zariya Alhaji Abubakar Tambuwal, Marafan Jere ...

     Marafan Jere kuma Dallatun Tafa Alhaji Abubakar Tambuwal.Daga Fatima Idris Zariya

Alhaji Abubakar Tambuwal, Marafan Jere kuma Dallatun Tafa a yayin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa dake garin Tafa karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna. Tunda fari ya yi addu'a ne ta musamman ga mai girma Gwamnan jihar Kaduna Malam Ahmed Nasiru El-Rufa'i.

Basaraken kuma ya yi jinjina sosai ga jama'ar jihar Kaduna musulmai da kiristoci wajalen amincewa da juna a bangaren zaman lafiya.

Alhaji Abubakar Tambuwal ya nuna kokarin da Sarakuna suke yi a bangaren samar da zaman lafiya a dukkan kasa baki daya. Don haka ne ma ya yi jinjina ga masarautan Jere karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Na Jeren. 

Ya ce ba ya ga sanin iya mulki da son jama'a na masarautarsa ta Jere ta bada damar kawo hanyar ci gaban yankin a bangarori daban daban musamman bangaren tsaro da harkar Ilmi da samawa matasa aikin dogaro da kai.

Basaraken ya yi misali da gagarumin sauyi da aka samu a garin Tafa a bangaren daidaita rayuwar jama'a.

Ya ce a lokutan baya garin Tafa ya yi kaurin suna da ya kai ga matafiya basa son tsayawa amma yanzu cikin ikon Allah da tallafawar Sarakuna da kungiyoyi masu zaman kansu komai ya canza. Bisa hakan ne Basaraken ya yi kira na musamman ga Gwamnatin jiha da na Tarayya da su karawa Sarakuna karfi domin magance sha'anin tsaro dake addabar Arewacin Nijeriya.

Ya ce idan Sarakuna suka sami karfi to tabbas tsaro zai samu a kasa baki daya ya ce idan aka duba Sarakuna sun fi kusa da jama'a don haka idan suka samu karfi to za a sami canji sosai.
 
Haka zalika Basaraken ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta kara fadin masarautar ta Jere domin ci gaban kasar ta Jere.

Ya ce bisa ga yawan jama'ar dake a kasar da karamar hukumar ya kamata a sami Karin masarautu. Ya ce hakan zai kara kawo hadin kai da samun ci gaban kasa.

Alhaji Abubakar Tanbuwal ya yi fatan alheri ga dukkan jama'ar masarautar Jere da Garin Tafa baki daya.

Shima Tafidan Marafan Jere Alhaji Garba Abdullahi mai shago a lokacin da manema labaran suka ziyarci fadar Marafan Jere ya yi godiya ne da addu'a ta musamman da masarautar ta Jere da fadar ta Marafan Jere Alhaji Abubakar Tambuwal, ya ce mutum ne mai kishin kasa da rayuwar al'umma.

Shima shugaban PCRC na yankin Tafa Malam Usman Abdul-Mumin shima ya jinjinawa fadar  mai girma Marafar Jere Alhaji Abubakar Tambuwal game da kishin kasa da al'ummar da yake tare da su kuma ya tabbatar da yana taimako ga al'umma baki daya.

Malam Zakariyya Alhasan na daga cikin malaman dake bayar da gudummwa a garin na Tafa shima godiya ya yi da ziyarar manema labarai fadar Marafan na Jere.

Karshe Limamin fadar Marafan na Jere Alhaji Abubakar Tambuwal, Malam Abdullahi Adamu ya yi addu'ar samun zaman lafiya ga fadar mai girma Marafan Alhaji Abubakar Tanbuwal da kasa baki daya.

Bincike ya tabbatar da cewa Alhaji Abubakar Tambuwal shi ya kawo makarantar Firamare a garin Tafa domin ci gaban al'umma.

Haka zalika Alhaji Abubakar Tambuwal bincike ya tabbatar da cewa shi ya kawo ofisoshin 'yan sanda na farko a garin Tafa dake karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

No comments