Shugaba Joe Biden na Amurka ya shaidawa taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Scotland cewa yaƙi da matsalolin dumamar yanayi a...
Shugaba Joe Biden na Amurka ya shaidawa taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Scotland cewa yaƙi da matsalolin dumamar yanayi abu ne mai matukar muhimmanci, da zai bada damar bunkasar tattalin arziki.
Ya kara da cewa kirkirar fasahar rage gurbatacciyar iskar da ake fitarwa zai samar da miliyoyin ayyuka a Amurka da sauran sassan duniya.
Daga nan kuma Mista Biden ya bukaci sauran kasashe su shiga tsarin da Amurka ta kaddamar da Tarayyar Turai, domin rage amfani da makamashi da ke gurbata muhalli da kashi 30 cikin 100.
" Mu yi alkawarin rage makamashin Methane a duniya, a dunkule mu rage gurbataccen sinadarin Methane da ake fitarwa da kashi 30 cikin 100 nan da shekara 10." Inji Biden
A lokacin bude taron a Glasgow, Firaminista Boris Johnson na Burtaniya ya gargadi shugabannin duniya cewa masu tasowa nan gaba ba za su taba yafe musu ba, idan har suka gaza wajen shawo kan matsalolin dumamar yanayi.
-BBC
No comments