Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kevin De Bruyne Na Manchester City Ya Kamu Da Korona

Gwaji ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiyar Manchester City Kevin de Bruyne ya kamu da cutar korona, bayan ya dawo daga buga wa...


Gwaji ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiyar Manchester City Kevin de Bruyne ya kamu da cutar korona, bayan ya dawo daga buga wa ƙasarsa Belgium wasa kamar yadda rahotanni suka labarto.

ÆŠan wasan mai shekara 30 ya killace kansa na tsawon kwana 10, wanda hakan ke nufin ba zai buga wasan da Manchester City za ta kara da Everton ba a ranar Lahadi, da kuma karawar gasar zakarun Turai da Paris St-Germain.

De Bruyne wanda aka yi allurar rigakafin korona a baya, ya ci wa Belgium ƙwallo a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya da ƙasarsa ta fafata da Wales a ranar Talata.

"Muna fatan alamomin ba su yi muni ba," in ji kocinsa Pep Guardiola.

"Ba za a daɗe ba zai dawo, ba za mu damu da irin girman giɓin da muka samu ba. Yana da muhimmanci sosai. Dole mu taimaka masa kuma muna fatan zai samu sauƙi yayin da ya killace kansa." Inji Guardiola.

No comments