Wani kwamitin bincike da gwamnatin jihar Legas ta kafa ya mika rahotonsa tare da cewa sojojin Nijeriya sun yi harbi tare da aika...
Wani kwamitin bincike da gwamnatin jihar Legas ta kafa ya mika rahotonsa tare da cewa sojojin Nijeriya sun yi harbi tare da aikata kisa kan masu zanga-zangar EndSars a shekarar da ta gabata kamar yadda BBC ta labarto.
Fitar rahoton kwamitin binciken ya karyata ikirarin da gwamnatin Tarayya ke yi na cewa babu wanda aka kashe a yayin zanga-zangar kamar yadda Ministan yada labarai da al'adu Lai Mohammed ke bayyanawa.
Dubban 'yan Nijeriya ne suka fantsama kan titunan kasar a watan Oktoban 2020 domin adawa da cin zarafin da sashen 'yan sanda na musamman SARS ke yi tare da kiran a kawo karshen rundunar.
Rahoton da ya fita a ranar Litinin, ya bayyana mutum 48 da lamarin ya shafa bayan sojoji sun bude wuta kan masu zanga-zangar.
Sai dai sojojin Nijeriyar sun musanta harba harsasai kan masu zanga-zangar.
Ita dai zanga-zangar #EndSars ta girgiza kasar kusan makwanni biyu. An zargi 'yan sandan da sata, da kai hari har ma da kisan mutane.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, da gangan sojoji suka yi harbi kan masu zanga-zangar a ranar 20 ga watan Oktoba a mashigar Lekki da ke birnin Legas.
Rahoton ya kuma gano cewa bayan sojoji sun gama na su harbe-harben, sai 'yan sanda suka ci gaba da far wa masu zanga-zangar tare da kokarin share duk wata shaida da za ta nuna sun aikata wani laifi ta hanyar kawar da gawawwaki, da kwashe harsasai.
Wasu daga cikin bayanan da rahoton ya gabatar dai sun zo daidai da wanda kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty ta fitar da kuma na kafafen yada labarai na ciki da wajen kasar suka ruwaito.
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, wanda shi ya kafa kwamitin, ya yi alkawarin amfani da shi da kuma tabbatar da an yi wa wadanda lamarin ya shafa adalci.
"Wannan rahoto zai ba mu damar fara abin da ya dace, duk da cewa cike yake da sarkakiya, za mu tabbatar da yin adalci ga wadanda abin ya shafa," in ji Sanwo-Olu.
Nan da makwanni biyu masu zuwa ne za a fitar da rahoton baki daya kamar yadda Mista Sanwo-Olu ya bayyana.
Yadda gwamnati ta tunkari batun zanga-zangar dai ya janyo allawadai daga kasashen duniya, lamarin da ya kai ga rusa rundunar 'yan sandan ta Sars.
Ita ma kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce hukumomin kasar sun ci gaba da cin zarafi da yi wa masu zanga-zangar da wadanda suka shirya ta barazana tun bayan aukuwar lamarin.
No comments