Korona Ta Kama Mutum 23 A Katsina


BBC ta labarto cewa; Hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Nijeriya ta ce an samu ƙarin mutum 110 da suka kamu da cutar korona a Nijeriya.

Alƙalumman sun nuna mutum 27 suka kamu da cutar a jihar Imo sai a jihar Katsina da aka samu mutum 23 a ranar Lahadi.

A jihar Rivers an samu mutum 20, sai jihar Ondo mai mutum 11. A Kaduna ƙarin mutum tara suka kamu da cutar.

Yanzu jimillar mutum 214,092 cutar ta shafa a Najeriya amma 207,254 sun warke yayin da cutar ta kashe mutum 2,976 a Nijeriya.

Ga jihohin da aka samu ƙarin cutar a Najeriya a ranar Lahadi.

Imo-27

Katsina-23

Rivers-20

Ondo-11

Kaduna-9

FCT-6

Oyo-6

Plateau-3

Osun-2

Ekiti-1

Gombe-1

Zamfara-1

Post a Comment

0 Comments