Ku Murkushe ‘Yan Bindigar Kan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna –Buhari Ga Jami’an TsaroShugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar da su kawo karshen barazanar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna, da ma sauran matsalolin tsaron da ake fuskanta a sassan kasar.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis din da ta gabata a karshen taron kwamitin tsaron Nijeriya, wanda ya gudana a karkashin jagorancin shugaba Buhari a Abuja.

Post a Comment

0 Comments