Hajiya Aishatu Laraba Abdulkadir Rashid A ranar Juma'ar da ta gabata ne kungiyar ci gaban kasar Dukku, 'Dukku C...
Hajiya Aishatu Laraba Abdulkadir Rashid
A ranar Juma'ar da ta gabata ne kungiyar ci gaban kasar Dukku, 'Dukku Community Progressive Association (DCPA)' ta ziyarci gadar Gombe Abba domin duba yanayin matsalar wannan gadar.
A yayin ziyarar, Shugabar kungiyar DCPA Hajiya Aishatu Laraba Abdulkadir Rashid ta mika ta'aziyyar kungiyar DCPA ga ilahirin iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sanadin lalacewar wasu bangarorin wannar gadar, sannan ta bayyana takaicinta da irin yadda gadar ta zama wani babban abin fargaba ga matafiya.
A wani bangaren kuma Kungiyar DCPA ta bayyana lalacewar robobin da ke a tsakiyar mahadar gadar, da lalacewar gefe-gefen hawa gadar a matsayin abin da ke kara jawo hatsaruruka a gadar. Sannan yawan hatsaruruka su suka jawo karyewar karafunan kan gadar.
A karshe kungiyar tana kira ga hukumomi, da sauran wadanda suke da ruwa da tsaki a wannan bangare na gyaran hanya da su taimaka su kawo ma al'umma dauki na gyaran wannan gada a cikin gaggawa kamar yadda Umar Babagoro, Jami'in hulda da jama'a na kungiyar ya tabbatar a wata sanarwar manema labarai da ya aikowa da MADOGARA.
No comments