Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyar HAYVA Ta Shirya Taron Wayar da Kan Masu Amfani Da Kafafen Sada Zumunta Na Zamani

Daga Abubakar M Taheer Hadejia. Kungiyar sa kai ta matasa masu Kishin kasar Hadejia (HAYVA) ta shirya taron wayar da kan matasa ...



Daga Abubakar M Taheer Hadejia.

Kungiyar sa kai ta matasa masu Kishin kasar Hadejia (HAYVA) ta shirya taron wayar da kan matasa masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani a dakin taro na UBJ Mall dake cikin garin Hadejia.

Taron wanda aka fara shi da yammacin ranar Litinin ya samu halartar masana, Malamai, masu Sarauta da matasa wanda aka gabatar da jawabai masu ratsa jiki kan amfanin kafafen sadarwa na zamani.

Malami A Kwalejin Ilimi dake Gumel Aji Kima Hadejia shi ne ya bayyana makasudin wannan taro da kuma lokacin da aka dauka ana tanadin wannan ranar.

Da yake jawabi shugaban Kungiyar Kuma Mamallakin Kamfanin UBJ Alhaji Umar Babuga Jibir ya bayyana cewa sun kirkiri wannan taro ne domin seta kalamai da rubutun matasan yankin musamman yadda suke amfani da su a wannan zamani.

Babuga ya kara da cewa kamata ya zama mqtasa sun yi amfani da kafafen sada zumunta domin samarwa da yankin ci gaba ba wai babatun kare wasu ba.

Alhaji Babuya ya nuna farin cikinsa kan yadda matasan suka nuna gamsuwarsu da jin dadinsu da wannan taron karfafawa da wayar da kai.

Shima a na sa jawabin wakilin Mai Martaba Sarkin Hadejia Muhammad Makama Shehu Dan Madamin Hadejia ya nuna farin cikinsa da gamsuwarsa kan wannan taron domin samar da ci gaba ga masarautar baki daya.

A karshe matasa sun bayyana jin dadinsu da gamsuwar su kan wannan taro da kuma fatan yin aiki da abubuwan da aka sanar musu a taro.

Wannan ne de karo na uku da kungiyar sa kai ta Garin Hadejia (HALVA) ta shirya wannan taro mai matukar muhimmanci a wannan Zamani.

No comments