Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama Na So Amurka, Birtaniya Su Sanya A Saki Fasfo Din Fita Kasashen Waje Na Shaikh Zakzaky Da Matarsa

  Kungiyar Hadin Kan Kare Hakkokin Dan Adam (CfHD) ta bukaci ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya da Canada da su taimaka tare da samar ...

 


Kungiyar Hadin Kan Kare Hakkokin Dan Adam (CfHD) ta bukaci ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya da Canada da su taimaka tare da samar da hanyar da za saki fasfon kasa da kasa na shugaban ‘yan shi’a Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Zeenah domin ba su damar fita kasashen waje neman lafiyarsu. 

A cikin wata sanarwa da Daraktan CfHD Dr Umar Abubakar na IMN ya fitar, a jiya, kungiyar ta ce gwamnati ba ta mayarwa shugaban ‘yan shi’ar fasfo dinsa na kasa da kasa ba tun bayan tafiya neman lafiya da aka yi zargin gwamnati ta kawo masa cikas a shekarar 2018.

Abubakar ya ce hukumar leken asiri ta Nijeriya, NIA da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) duk sun musanta mallakar takardun fita kasashen waje na ma’auratan tun bayan da aka sake su biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun Kaduna ta yanke.

An tsare mutanen biyu ne sama da shekaru biyar kuma inda aka tuhume su da laifin kisan kai da dai sauran tuhume-tuhume biyo bayan wata arangama tsakanin ‘yan IMN da sojoji a Zariya ta jihar Kaduna a watan Disambar 2015.

Wata babbar kotun jihar Kaduna da ke zamanta a gaban Mai Shari’a Gideon Kuradah, ta yanke hukuncin ne a ranar 28 ga watan Yuli, 2021, ta ce gwamnatin Kaduna ta gaza gabatar da hujjoji a kan wadanda ake kara, a don haka ta sallame su tare da wanke su baki daya.

Sai dai bayan an sake su, gwamnatin jihar ta shigar da wasu sabbin tuhume-tuhume a gaban babbar kotun tarayya da ke da alaka da ta’addanci da kuma cin amanar kasa.

CfHD ta koka da cewa “watanni uku bayan sallamar da wata babbar kotun jihar Kaduna ta yi wa El-Zakzaky da matarsa, har yanzu ba su je kasar waje neman lafiya ba saboda har yanzu fasfo dinsu na kasashen waje na hannun jami’an tsaro kuma ba a bas u wani sabon fasfo ba”.

"Hukumar leken asiri ta Nijeriya (NIA) da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun musanta rike fasfo din kasashen waje na ma'auratan."

Sanarwar ta yi zargin cewa, a lokacin da suka fita zuwa kasar Indiya shekaru uku da suka gabata, “kamar yadda babbar kotun Kaduna ta bayar da umurni, wadannan jami’an tsaro sun kwace takardun fita na kasa da kasa isar su ke da wuya.

“Muna fatan wannan ba wani mugun shiri bane na wadanda suke rike da madafun ikon  Nijeriya domin hana ma'auratan samun kulawar neman lafiya.”

Abubakar ya ce kimanin shekaru shida ke nan da rahotannin likitoci suka nuna cewa halin lafiyar jagoran addinin musuluncin da matarsa sun tabarbare kuma suna bukatar tafiya kasashen waje domin neman magani.

“Wannan dalilin ne ya sa babbar kotun jihar Kaduna ta ba su damar fita jinya wanda gwamnati ta kawo wa tafiyar cikas a shekarar 2018.

“Hadakar kungiyar kare hakkin bil’adama da sauran masu son adalci a fadin duniya sun sake tada jijiyoyin wuya saboda wadannan munanan abubuwan da suka faru ciki har da kamar ma gwamnati na ci gaba da tsare mutanen biyu ne a gida.

"Saboda haka, muna kira ga al'ummar duniya musamman gwamnatocin Amurka, Birtaniya da Kanada da su tursasawa gwamnati ta saki fasfo din Shaikh Zakzaky da matarsa," in ji Abubakar.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta sako musu fasfo din su ko kuma ta ba su sababbi, wanda hakan zai ba su damar zuwa asibitin da suke so ba tare da bata lokaci ba.


No comments