Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyar Matasan Arewa Sun Karrama Wasu Manyan Mutane A Arewa

      Hoto: Alhaji Abdul Aziz Husaini Sarkin Fadan Sarkin Gidi Moni yayin da yake ganawa da manema labarai bayan karbar kambun k...

      Hoto: Alhaji Abdul Aziz Husaini Sarkin Fadan Sarkin Gidi Moni yayin da yake ganawa da manema labarai bayan karbar kambun karramawa daga hanun wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli a dakin taro na Arewa House dake Kaduna.


Daga Fatima Idris Zariya

A cikin mako da ya gabata ne kungiyar matasan Arewa wato 'Northern Youth Coucil of Nigeria ( NYCN)' ta gudanar da taron karawa juna sani da karrama wasu manyan mutane bisa gudummawar da suke bayarwa ga al'umma.

Taron ya gudana ne a babban dakin taro na Arewa House dake garin Kaduna.

Taron ya sami halartar manyan mutane daga bangarori daban daban ciki da wajen jihar ta Kaduna.

Mahalarta taron sun hada da Sarakuna da manyan 'yan siyasa da shuwagabannin cibiyoyi gami da shugabannin tsaro na ciki da wajen jihar.

Daga cikin abin da aka tattauna a wajen taron ya hada da kalubalen da matasa ke fuskanta da kuma tsaiko da kasarmu take samu a bangaren tattalin arzikin kasa a wannan lokacin.

Bayan haka 'ya'yan kungiyar ta (NYCN) sun karrama wasu manyan mutane da suka yi wa kasa hidima a bangarori da dama.

Daga cikin wadanda aka karrama akwai matashin Basarake Alhaji Abdul-Aziz da mutane kusan 10 daga bangarori daban daban.

Bayan kammala taron wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin Alhaji Abdul-Aziz wanda kunyiyar ta ba shi sarautar Garkuwar matasan Arewa a wannan ranar.

Alhaji Abdul-Aziz Husaini Sarkin Fadar Sarkin Gidimoni kuma Garkuwar Matasan Arewa ya fara ne da mika godiya ga Allah da ya nuna masa ranar da aka karrama shi bisa wasu kyawawan ayyukan da yake gudanarwa ga al'umma.

Basaraken ya kara da mika godiyarsa ga wakilan mai Martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli bisa kasancewarsu a wajen taron.

Kuma ya yi godiya ga kungiyar da ta karrama su  ta bashi mukamin Garkuwa matasan Arewa kuma ya ce hakan ya kara mishi kwarin guiwa akan dukkan abin da yake yi ga al'umma. 

Kuma ya yi fatan yadda kowa ya zo taron lafiya Allah ya mai da kowa gida lafiya.

Daga karshe 'ya'yan kungiyar sun yi wa manema labarai fashin baki game da dalilinsu na shirya taron gami da bayar da karamcin ga wasu daga cikin manyan bakin da suka halarci taron. 

Kwamared Awwal el-Tinkzz Aliyu na daya daga cikin shuwagabannin kungiyar ta NYC.

Kwamared ya fara ne da godiya ga Allah tare da jinjina mai yawa ga dukkan manyan bakin da suka sami halartar taron na su musamman Sarakuna da 'yan siyasa da shugabannin cibiyoyi da jami'an tsaro bisa namijin kokari da suka nuna na halartar wannan taro.

Baya ga haka Kwamared Awwal ya bayyana ra'ayin su na shiya taron da cewa, taro ne na neman mafita ga kasarmu Nijeriya ta bangaren halin da matasa ke ciki da yadda za a samo mafita a bangaren tattalin arzki kasa da kalubaken dake da ake fuskanta.

Baya ga haka ya ce kungiyar ta su ta karrama wasu mutane masu kwazo wajen taimakawa al'umma da kasa baki daya wanda suka yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da halayen wanda suka karrama.

Karshe Kwamared Awwal ya yi fatan shawarwarin da masu mukala suka bai wa gwamnati da fatan za tayi amfani da shi.

Haka zalika ya yi fatan dukkan mahalarta taron za su yi amfani da abin da suka ji a wajen taron tare da fatan Allah ya maida kowa gida lafiya.

No comments