Daga Bello Hamza, Abuja da Isah Abdullahi, Zariya Abin al’ajabi da ban takaicin da ya faru na wasu dangi makusanta da suka yi la...
Daga Bello Hamza, Abuja da Isah Abdullahi, Zariya
Abin al’ajabi da ban takaicin da ya faru na wasu dangi makusanta da suka yi lalata da wata yarinya kafin aurenta, a garin Soba da ke yankin Zariya ta Jihar Kaduna, ya yi matukar daga hankulan jama’a, kasancewar Zariya yanki ne da ake tunkaho da shi a matsayin shalkwatar ilimin addinin musulumci da kuma na zamani.
Saboda tarin malaman da kasar Zazzau ta yi shuhura da su masu gyaran zuciya da nesantar kazantar duniya, galibin mutanen yankin sun samu shaidar jin tsoron Allah wandanda koyarwar addini ta yi tasiri a rayuwarsu, amma labarin abin da ya faru a wani kauye da ke yankin garin Soba mai suna Unguwar Shafifa ya sabbaba alamomin tambaya kan irin yadda dabi’un mutanen da aka sani da riko da addini ke sauyawa zuwa abar kyama.
Tabbas, ba zai yiwu a ce dukka an zama daya ba, amma dai an ce wake daya ke bata gari. Wannan al’amari da ya faru a cikin dangi daya, makusanta a Unguwar Sharifai ta yankin Soba ya fito da yadda tabarbarewar tarbiya da badala ta mamaye yankunan karkara. A da akan fi tunanin fasadi na zinace-zinace da shaye-shaye sun fi yawaita a birane amma a wannan karon, sai ya zamo ana zaton wuta a makera sai ga ta a masaka.
Yadda wannan lamari ya faru kuwa shi ne, wata yarinya mai suna Aisha Ayuba ‘yar shekara 16 a duniya wadda ke zaune da iyayenta a kauyen na Unguwar Sharifai, ta kasance tana gudanar da harkokin rayuwarta ta sha’awa a boye har zuwa lokacin da aka sa mata ranar aure da masoyinta Abdullahi Hamisu. Kamar yadda al’ada ta tanada, shi Abdullahi Hamisu yana zuwa tadi gidan yarinyar a kai-a kai, amma wani abin da ya saba wa al’adar zance har ma da tsarin addini a kasar Hausa shi ne, a she duk lokacin da ya je tadin yakan ribaci Aisha, daga tabe-tabe har ya kai ga yana kwanciya da ita. Haka suka yi ta yi har aka daura musu aure, kowa na farin ciki, amma ana wata bakwai da daura auren sai Aisha ta haihu a ranar 13 ga watan Oktobar 2021. Maimakon murna da samun karuwar haihuwa sai reshe ya juye da mujiya, inda lamarin ya tayar da hankalin mijin da iyayensa, ba tare da wata-wata ba suka tasa keyar mai jego zuwa gidansu, domin a cewarsu, cikin ba na Abdullahi mijinta ba ne, hasali ma an yi musu ungulu da kan zabo, saboda an aura masa ita ce da cikin shege.
Wannan dambarwar ta kai ga dunguma zuwa gidan Sarkin Unguwar Sharifai, Alhaji Zubairu don neman mafita, musamman ganin Abdullahi ya ce, ba shi ya yi wa Aisha ciki ba. Binciken da iyayen Aisha da fadar sarkin garin suka gudanar ya kai ga bankado ta’asa mai matukar tayar da hankali, wadda ta kara fito da yanayin tabarbarewar tarbiyya da yaduwar badala a yankunan karkara, inda yarinyar ta bayyana yadda wasu ‘yan uwanta suka yi ta kwanciya da ita a lokutta daban-daban kafin ta yi aure. Ta lissafo mutum uku bayan shi mijin nata, da suka yi wannan aika-aika da suka hada da wanta da suke uwa daya uba daya Zubairu Sha’aibu, da wan mijinta Umar Hamisu da kuma mijin yayarta Ibrahim Abdulkadeer Kan Kuda.
Aisha ta yi bayani dalla-dalla yadda wadannan mutane dangi makusanta suka yi ta yaudararta suna amfani da ita, kuma abin takaicin shi ne ba ta iya tantance wanda yake da alhakin yi mata cikin da take dauke da shi ba, har ta kai ga ta haifi danta namiji.
Wani babban lamari da ya fi daukar hankali kan wannan abin kyama shi ne yadda al’umma suka kasa fahimtar ta yaya wan Aisha, Zubairu ya iya kawar da ‘yan’uwantakar da ke tsakaninsu har sha’awa ta zo masa kuma ya kasa dannewa har ta kai shi ga lalata da kanwarsa uwa daya uba daya, wannan jaraba ce ko alkaba’i? Haka nan, me ya sa mijin yarta Ibrahim Abdulkadeer Kan Kuda ya cire kunya da tsoron Ubangijin Al’arshi ya fadawa kanwar matarsa alhali yana tare da yayar ba su rabu ba?
Wasu masana halayyar bil’adama dai na ganin cewa, wannan lamarin ya kai kololuwar lalacewar tarbiyya a tsakanin al’umma, ya kuma kamata malamai da mahukunta su zage damtse wajen gangamin wa’azi da fadakarwa don ceto al’umma daga halaka. Domini dan aka ci gaba da bari mace da namiji uwa daya uba daya suna lalata da juna, to nan gaba, ba a san me zai faru ba, kuma duk ire-iren wannan badalar c eke kara wargaza zaman lafiyar al’umma.
Bayan da aka samu wadannan bayanai daga binciken da aka gudanar a fadar Sarkin Unguwar Sharifai, sai aka dunguma zuwa babban ofishin yanki na ‘yan sanda da ke garin Soba inda bayani ya nuna cewa, bayan tattaro dukkan wadanda Aisha ta bayyana cewa, sun yi lalata da ita, suka kuma tabbatar da cewa, ba sharri ta yi musu ba, sai aka umarci gudanar da gwajin kwayar halitta don tantance wane ne asalin uban yaron da aka haifa.
Abin mamaki, kowa ya amince da yin haka sai mijin Aisha, Abdullahi Hamisu ne kadai ya tubure, ya ki bayar da hadin kai, ya ce bai yarda ba, kuma aka nemi ya karbi yaron, nan ma ya ce atafau! ba zai karbi yaron ba.
Majiyarmu a ofishin ‘yan sandan garin Soba ta bayyana mana cewa, babban jami’in ‘yansandan yankin ya janye hannunsa daga wannan kitimirmirar. Inda ya shawarce su gaba daya su mika kokensu zuwa kotu, don a cewarsa, ba shi da hurumin ci gaba da bibiyar lamarin zuwa yanke hukunci, don lamari ne da ya shafi hulda a tsakanin fararen hula ‘Cibil Case’. A halin yanzu dai Aisha na can da danta da ba wanda ya karbe shi a matsayin da sai ita da ya zama mata dole, su kuma wadanda suka aikata badalar da ita suna can sun ci gaba da gudanar da harkokinsu, ba mamaki ma wannan bai ishe su izina ba.
To, wai shin a musulunce mene ne matsayin wannan auren da aka daura tsakanin Aisha da Abdullahi tun da farko da kuma matsayin yaron da aka haifa? Wani shehin malami a garin Samarun Zariya, Malam Muhammad Lukman Alfa, ya amsa da cewa, “A shari’ance kasantuwar an yi fasikanci da wata bai hanawa a aureta, sai dai malamai sun togace a kan cewa, sai in ciki bai bayyana ba, amma in har an samu bayyanar ciki to lallai babu aure a tsakaninsu kwatakwata amma wasu mazahabar kuma suna ganin za a iya yin auren, shi kuma yaro yana nan a matsayin da ga mijin yarinyar tunda cikin ya kai wata bakwai a gidansa, domin a shari’ance ana iya haihuwar yara a cikin wata bakwai, sannan tunda akwai hanyyoyin zamani na tantance waye uban yaro, ana iya bi.”
Malam Lukman ya kara da cewa, “Wannan kwamacalar tana kara nuna raunin addini da imanin al’ummarmu a wannan lokacin ya kuma kara fito da bukatar a rungumi tarbiyya da addinin musulunci ya koyar da mu, musamman abin da ya shafi rarraba wurin kwanciyar yara, don abu ne mai tayar da hankali na cewa, wanta uwa daya uba daya yana daga cikin wadanda suke lalata da ita, idan ka bibiya kana iya samu sun samu cundanya da juna ne a wani mataki na tasowarsu. Dole mutane su koma wa shari’a don kauce wa faruwar irin wannan fitinar,”.
Ya kuma nemi iyaye su kula da tarbiyar yaransu ta hanyar kai su makaranta don a makaranta ce ake samun cikakkiyar tarbiyya. Har ila yau ya nemi a rika gaggauata aurar da ‘yan mata don kauce wa yaduwar fasadi a tsakannin al’umma.
A halin yanzu dai Aisha na can babu aure babu uban da.
No comments