Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Lai Mohammed Ya Yi Watsi Da Rahoton Binciken ‘Kisan Kiyashin Endsars’

Ministan yada labarai da al’adu na Nijeriya Lai Mohammed, ya yi watsi da rahoton kwamitin bincike da gwamnatin jihar Legas ta ka...


Ministan yada labarai da al’adu na Nijeriya Lai Mohammed, ya yi watsi da rahoton kwamitin bincike da gwamnatin jihar Legas ta kafa kan zargin 'kisan kiyashi' da aka yi a kofar shiga Unguwar Lekki.

A wani taron manema labarai da ya kira a Abuja a yauTalata, Ministan ya kira rahoton a matsayin “jaddada labaran ƙarya da ake yaɗa wa a kafofin sadarwa na Intanet tun lokacin da al’amarin ya faru a watan Oktoba", kamar yadda ya shaida.

“Mun yi watsi da batun cewa sojojinmu da ƴan sanda sun hallaka ƴan Nijeriya da ba su ba ji ba ba su gani ba a Lekki a ranar 20 ga watan Oktoban 2020,” in ji Lai Mohammed.

Ministan ya ƙara da cewa zargin kisa ba ƙaramin abu ne wanda ba zai dogara kaɗai ba akan zargi yana mai cewa an fitar da rahoton ne da ke yawo a kafofin sadarwa don a kunyata gwamnati da kuma hukumominta ba tare da hujjoji ba.

Ya ce gwamnati ba za ta taɓa bari hukumominta na tsaro su ci zarafi ko keta haƙƙin ƴan Nijeriya ta ko wacce irin hanya, “dalilin da ya sa aka soke SARS tare da ƙarfafawa jihohi su kafa kwamitin bincike kan rahotannin take haƙƙin ɗan Adam da ake zargin ƴan sandan SARS sun yi.

No comments