Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

LINA MEDINA: Yadda ‘Yar Shekara Biyar Ta Zama Mahaifiya Mafi Kankantar Shekaru A Tarihi

Daga Muhammad A. Dalhatu Lina Medina tana da shekaru biyar da wata bakwai da kwanaki ashirin da daya a duniya ta haihu. Wanda ha...


Daga Muhammad A. Dalhatu

Lina Medina tana da shekaru biyar da wata bakwai da kwanaki ashirin da daya a duniya ta haihu. Wanda hakan ya maisheta mahaifiya mafi kankantar shekaru a tarihi. Hakan ya faru ne sakamakon yanayin halittarta da a turance ake ce ma ‘precocious puberty’ wanda masana suka fassara da cewa yanayin halitta ne da ke sanya mai kananan shekaru jikinsa ya sauya zuwa na masu shekaru da wuri. Wanda wannan dalilin ne ya sanya ta samu juna biyu har ta haihu tana da kananan shekaru. Hakan dai ya zama abin mamaki da mu’ujiza a tarihin ma’abota kiwon lafiya.


A cikin  watan Afrilun 1939 mahaifiyar Lina Medina ta dauke ta ta kaita asibiti a Pisco dake kasar Peru, domin ganawa da fitaccen Likitan nan Dr Gerardo Lozada domin ya taimaka mata.

Mahaifiyarta ta fara lura da yadda ‘yarta cikinta ya fara kumbura, inda hakan ya da ga mata hankali duba da yadda ta fito daga wani kauye ana ce masa Andes. Mahaifiyarta a zatonta aljanu ne suka shafi ‘yarta suke kuma juya jikin ‘yarta din. Ganin yadda jikin ‘yar ke kara girma ba ta yadda aka saba gani ba.

Da farko Dr Lozada ya dauka wata nau’in cuta ce da ke sanya mutum kumbura, amma domin tabbatar da hasashensa, likitan sai ya dan yi wadansu bincike da gwaje-gwaje yarinyar mai shekaru biyar a duniya. Bisa mamakinsa sai ya lura da kamar ‘yar na dauke da wata ‘yar a cikinta saboda yadda ya ji bugun zuciyarta.

Domin tabbatar da bincikensa, Dr Lozada ya dauke ta zuwa Lima wato Babban birnin Peru domin ganawa da wadansu likitocin. Sai ko bincikensa ya tabbata, inda aka same ta tana dauke da juna biyu har na tsawon wata bakwai.

A ranar 14 ga watan Mayun 1939, tana da shekaru biyar da wata bakwai da makonni uku a duniya, Lina Medina ta kasance mahaifiya mafi kankantar shekaru a tarihi da ta haihu. An haifi yaron cikin koshin lafiya inda nauyinsa ya kai kilogiram 2.7. Wanda hakan ya zama sabon abu a duniyar kiwon lafiya a duniya. Inda lamarin ya zama abin mamaki babba!


Lina Medina ta haihu ne bayan da aka yi mata tiyata, sakamakon ba za ta iya haihuwa da kanta ba. Inda kuma aka yi nasarar yin tiyatar ba tare da samun wata tangarda ba. An sanyawa jaririn suna da Gerardo, inda ya ci sunan likitan da ya yi wa mahaifiyarsa tiyata har aka haife shi.

Haihuwar da Lina ya sanya ya zama abin tattaunawa a kasa baki daya. Inda aka sake yi mata gwaji, inda gwajin ya nuna cewa tana da halittarnan ta ‘precocious puberty’, wani irin nau’in halitta dake sanya mai kananan shekaru girma da wuri. Lamarin na aukuwa sau daya cikin yara dubu goma. Inda a zahiri gabanta ke kammala girma da cika.

Binciken da aka sake yi ya nuna cewa Lina Medina ta fara al’adarta na farko tun tana da shekaru uku a duniya. A shekaru hudu kuma, nononta ya fara girma, inda tana da shekara biyar jikinta ya nuna alamar manyantaka inda kashinta suka kara karfi.

Tambayar da mafi yawan mutane za su so a amsa musu a nan shi ne; wa ya yi mata cikin?

Da farko hukumomin kasar Peru sun yarda da cewa daga cikin iyalinta ne ko ‘yan’uwanta wani ya sadu da ita. Wanda bisa wannan dalilin aka kama mahaifinta bisa zargin cin zarafin ‘yar. Sakamakon rashin samun gamsasshiyar hujja bisa zargin da ake yi masa, aka sake shi daga baya.

Har ya zuwa yau, an kasa gano wane ne mahaifin yaron sakamakon Lina ta yi kankantar da za ta iya sani.

Iyayen Lina ne suka reni ‘yarsu da jikansu wato Gerardo a tare, wanda yaron tun tasowarsa ya dauka Lina ma yayarsa ce. Sai da ya kai shekara goma a duniya sannan a ka gaya masa cewa mahaifiyarsa ce ita.

Dr Lozada ya ci gaba da taimakon Lina da dan da ta Haifa, inda tun Lina tana budurwa likitan ya dauke ta aiki a ofishinsa yana biyanta albashi. Inda har ta samu ta yi karatu ita da abin da ta Haifa wato Gerardo.  

Daga bisani Lina ta auri wani mai suna Raul Jurado inda ta haihu da shi a shekarar 1972. Inda Gerardo, yaron farko da ta Haifa a lokacin ya kasance yana da shekara 33 a duniya sannan ya samu kani.


Gerardo ya rasu yana da shekara 40 a duniya sakamakon cutar bargon kashi. Dr Lozado ya ce abin da ya faru da Lina Medina har ta zama mahaifiya mafi kankantar shekaru a tarihi, abu ne da ya ba shi mamaki wanda ya faru a tarihin aikinsa, kuma wani lamari da aka kasa magance shi a tarihin sha’anin kiwon lafiya. 

-Rahoton MADOGARA

No comments