Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MAAUN Ta Mika Ta'aziyya Ga Iyalai Da Gwamnatin Katsina Bisa Rasuwar Tsohon Ministan Noma

Hukumar gudanarwar ta Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), ta jajantawa gwamnatin jihar Katsina da iyalan tsohon m...Hukumar gudanarwar ta Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), ta jajantawa gwamnatin jihar Katsina da iyalan tsohon ministan noma, Abba Sayyadi Ruma wanda ya rasu a birnin Landan bayan gajeruwar rashin lafiya a ranar Larabar makon jiya.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wanda ya kafa kuma shugaban Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya raba wa manema labarai a Kano a ranar Talata.


Farfesa Gwarzo ya bayyana rasuwar tsohon ministan a matsayin babban rashi ba ga iyalansa da ‘yan'uwa da abokan arziki ba har ma da kasa baki daya.

Ruma ya kasance ministan noma a zamanin Marigayi shugaba Umaru Musa Yar’adua.

Ya bayyana Marigayin a matsayin mutumin kirki wanda ya yi iya bakin kokarinsa a matsayinsa na ministan noma wajen kawo sauyi a fannin.

"A madadin daukacin ma’aikata da hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga ‘yan'uwa da abokan arziki da ma gwamnatin jihar Katsina bisa rasuwar tsohon Ministan.

"Allah ta’ala ya gafarta masa kurakuransa, ya bai wa iyalansa hakurin jure rashin,” inji shi a cikin sanarwar.

Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu a Afirka, ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya sanya Marigayin a Aljannar Firdaus sannan ya bai wa iyalansa hakurin jure rashin da ba za a iya mayarwa ba.

Marigayin wanda ya rasu yana da shekaru 59 a duniya, tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

No comments