Mahara Sun Yi Wa Magidanci Da Matarsa Kisan Gilla A Jigawa

                  Marigayi Alhaji Musa

Daga Muhammad Farouk

Wadansu da ake zargin masu kisan kai ne sun yi wa wani magidanci da matarsa kisan gilla a karamar Hukumar Malam Madori ta jihar Jigawa kamar yadda majiyarmu ta labarto. 

Ma'auratan wanda aka bayyana da Alhaji Musa da Hajiya Adama an kashe su a daren ranar Asabar da misalin karfe 2:30. 

Kakakin 'yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa wadanda ake zargi da kisan kan sun farmaki gidan Marigayin ne a Kauyen Kebberi inda suka harbe su dukkansu. 

Kakakin ya ci gaba da cewa; wadanda ake zargi da kisan kan ba su dauki komai daga wanda suka kashe ba, wanda yake Manaja ne a Kamfanin 'Three Brothers Rice Mill' a Hadeija. 

"A ranar 13 ga watan Nuwamba, wadansu da 'yan ta'adda suka haura gidan wani mai suna Alhaji Musa, Manaja a Kamfanin 'Three Brothers Rice Mill, inda suka harbe shi da matarsa Hajiya Adama duk a Kauyen Kebberi a karamar Hukumar Malam Madori", Shiisu ya tabbatar. 

Ya tabbatar da cewa sun samu wayar hannu guda biyu a inda aka yi kisan, sannan ana binciken mutum biyar da ake zargi. 

Shiisu ya tabbatar da cewa suna kokari cafko wadanda suka tsere bayan aikata barnar. 

Post a Comment

0 Comments