Majalisa Ta Amince Wa Shugaba Buhari Ya Ciwo Bashin Dala Biliyan 16.2

 


Majalisar Dattawa ta amince wa Shugaba Muhammadu Buhari ya ciwo bashin dala biliyan 16.2.

Majalisar ta amince da buƙatar ciyo bashin ne bayan da Shugaba Buhari ya gabatar mata kudurin hakan a watan Mayu, kuma bashin yana cikin tsarin ciwo bashi na 2018 zuwa 2020 na gwamnatin Tarayya.

Majalisar ta amince da buƙatar ne a zamanta na ranar Laraba.

Amincewar ta biyo bayan la'akarin da majalisar ta yi ne da rahoton kwamitinta a kan basussukan cikin gida da na waje.

Post a Comment

0 Comments