A yau Talata manyan kungiyoyin Turai ke komawa fagen fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai a matakin kungiyoyi 16, inda hankula suka ka...
A yau Talata manyan kungiyoyin Turai ke komawa fagen fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai a matakin kungiyoyi 16, inda hankula suka karkata kan Manchester United da Barcelona.
Wasan da Barcelona za ta yi da Benfica na cikin masu daukar hankula ganin cewa, zai zama babban zakaran gwajin dafi ga sabon kocinta Xavi Hernandez wanda aka dora wa alhakin ceto kungiyar ta Barcelona daga halin koma-bayan da take fuskanta.
Wasan na yau zai fayyace makomar Barcelona dangane da ci gaba da fafatawa a gasar ta zakarun Turai ko kuma akasin haka.
RFI ta labarto cewa; kodayake kocin ya samu nasara akan Espanyol da ci 1-0 a wasansa na farko da ya jagoranci kungiyar, abin da ya sa Barcelona ta dare zuwa mataki na 6 a teburin gasar La Liga ta Sipaniya.
Ita ma Manchester United za ta yi wasanta na farko tun bayan da ta sallami kocinta Ole Gunnar Solksjaer, inda za ta hadu da Villareal a gasar ta zakarun Turai a yau.
Daya daga cikin kalubalen da Manchester United ke fuskanta shi ne yadda take da tarin ‘yan wasa masu fama da rauni da suka hada da Paul Pogba da Raphael Varane baya ga kuma Luke Shaw da shi ma ake ganin ya samu buguwa a kansa a wasansu da Watford.
Sannan ga Mason Greenwood da gwaji ya nuna cewa, ya kamu da cutar Korona, sai kuma Edison Cavani wanda shi ma ake tababar taka ledarsa a yau saboda raunin.
No comments