Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Manoman Nijeriya Na Amfani Da Maganin Kwarin Da Aka Haramta A Turai - Rahoto

Wani bincike a Nijeriya ya ce manoman kasar na amfani da magungunan kashe kwari masu matukar illa wadanda aka haramta sayar da s...


Wani bincike a Nijeriya ya ce manoman kasar na amfani da magungunan kashe kwari masu matukar illa wadanda aka haramta sayar da su ko amfani da su a kasashen Turai saboda illar da suke yiwa Bil Adama.

Binciken da kungiyar dake yaki da maganin kwari a gonaki ta gudanar wanda ya samu tallafin kungiyar Heinrich Boll Stiftung ya ce kashi 40 na magungunan kashe kwarin da ake amfani da su a gonakin Nijeriya tuni aka haramta amfani da su a kasashen Turai.

Rahotan binciken da aka yi a Jihohin Kano da Oyo da Ebonyi da kuma Binuwe ya ce adadin kashi 40 din da aka gabatar na nuni ne da kashi 57 na nau’in abincin daban-daban da suka kai kala 402 da ake nomawa a cikin Nijeriya.

Binciken ya ce akasarin maganin kwarin na dauke da sinadaran dake matukar illa ga rayuwar Bil Adama da dabbobi da kuma muhalli.

Rahotan ya ce kashi 25 na magungunan kwarin da aka yi wa rijista a Nijeriya na da sinadarin dake iya haifar da cutar kansa ko kuma sankara, yayin da kashi 63 na da sinadarin dake haifar da cuta a jikin Bil Adama, sai kuma kashi 47 da ke dauke da sinadarin dake haifar da matsala a jinin Bil Adama.

Binciken yace magungunan kwarin 262 na dauke da guba, yayin da 224 suka nuna yadda suke haifar da matsalar rashin haihuwa.

Rahotan masanan ya ce an gano illar da irin wadannan magunguna kan yi wa muhalli lura da yadda mutane 270 suka mutu sakamakon gurbata ruwan su da irin wannan maganin kashe kwarin da aka haramta amfani da shi a nahiyar Turai ya yiwa mutanen Jihar Binuwe.

Jaridar Premium Times ta ruwaito masanan na bada shawarar cewar ya dace majalisar dokoki ta kasa ta kaddamar da bincike akan matsalar da zummar yin dokar da zata takaita amfani da irin wadannan magungunar dake yiwa jama’a da muhalli illa.

(RFI)

No comments