...sun riƙe guda uku sai an kai musu babura 3 Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kaduna ta tabbatar da sakin 10 da ga cikin 13 na ma...
...sun riƙe
guda uku sai an kai musu babura 3
Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kaduna
ta tabbatar da sakin 10 da ga cikin 13 na ma'aikatan ƙaramar hukumar Zariya da
ke Kaduna.
Mohammed Jalige, Kakakin rundunar,
shi ne ya shaidawa manema labarai a Zariya a yau Lahadi, inda ya ce tun a jiya
Asabar a ka sake su kuma an ci gaba da ƙoƙarin sakin sauran ma'aikata guda uku.
Sai dai kuma Jalige, mai muƙamin
ASP, ya ƙi ya faɗi ko an biya kuɗin
fansa kafin sakin ma'aikatan.
Amma kuma wata majiya da ta nemi a
sakaya sunanta ta shaidawa Kamfanin Daillancin Labaran Nijeriya, NAN cewa
ma'aikatan sai da su ka biya naira miliyan 40 sannan a ka sako su.
Majiyar ta ƙara da cewa ƴan uwan waɗan
da a ka yi garkuwa da su ɗin nen su ka haɗa kuɗaɗen.
Ta ƙara da cewa kuma masu garkuwa da
mutane ɗin ba su saki sauran mutum uku ba saboda sharuɗɗan da su ka gindaya
bayan an biya miliyan 40 ɗin nan shi ne cewa za su rike mutum uku har sai an saya
musu baburura guda uku sabo fil.
No comments