Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana damuwa akan yadda zaman lafiya ya gagari kasashen Afirka da dama, matsalar da ya ...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana damuwa akan yadda zaman lafiya ya gagari kasashen Afirka da dama, matsalar da ya ce tana yi wa nahiyar tarnaki wajen ci gaban ta.
Buhari wanda ke bude taron kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka karo na 9 a Abuja, ya ce ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun ci gaba da haifar da matsalolin dake raba mutane da muhallan su da kuma sake jefa su cikin kangin talauci.
Shugaban ya ce babu tantama mata da yara ne suka fi shan radadin illar dake tasowa daga matsalar rashin zaman lafiya, saboda haka ya bukaci matan shugabannin Afirka da su taimaka wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya.
Buhari ya bayyana farin cikinsa da yadda taron matan shugabannin ke aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma hadin kai ta hanyoyi daban-daban a kasashen su, yayin da ya bukaci taimaka musu wajen cimma muradun su na tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Daga karshe Buhari ya yabawa Uwargidansa Aisha akan kokarin da ta yi wajen mallakar filin da za a gina Sakatariyar kungiyar a Abuja, yayin da ya bayyana fatar ganin an yi amfani da ita wajen samarwa matasan ayyukan da za su dogara da kan su.
Matan shugabannin sun zabi Aisha Buhari a matsayin sabuwar shugabar kungiyar.
No comments