Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MUKALAR ALHAMIS: Gaskiya A Mahangar Mutane -Daga Umar Shuaibu

"A al'amurra na Hankali, dokar wanda suka fi rinjaye su ke da gaskiya ba ta da mazauni."  -Mahatma Gandhi.  Akwai ...


"A al'amurra na Hankali, dokar wanda suka fi rinjaye su ke da gaskiya ba ta da mazauni." -Mahatma Gandhi. 

Akwai abubuwa da dama da idan muka musu duba na tsanaki za mu ga cewa, Mutanen da suka rayu a wannan Duniyar Shekaru aru-aru da suka shuɗe ba su da bambanci da mutanen da ke rayuwa a wannan zamanin da ake tinkaho da cewa Ɗan Adam ya ci gaba a fannoni daban-daban na Ilimi. 

Daga cikin waɗannan abubuwan akwai tunanin cewa gaskiya na tare da mutanen da ke da rinjaye (yawa) ne, Ƙarya kuma na tare da 'yan kaɗan da suka saɓa da su. 

Duk da cewa a rayuwar mu na yau da kullum muna ganin saɓanin wannan Tunani na mafi yawan mutane, kuma masana da dama sun yi biji-biji da wannan mahangar da dalilai masu karfi na hankali a lokuta daban-daban. Amma har yanzu da yawan mutane na ci gaba da ƙaryata ko gaskata al'amurra bisa dogaro da wannan tunanin. 

Bertrand Russell, masanin ilimin Falsafa da lissafi yana cewa: kasancewar an yi riƙo da wani ra'ayi a ko'ina, ba shi zai tabbatar da cewa wannan ra'ayin ba shirme ba ne; hakika bisa la'akari da wautar yawancin 'yan adam, irin wannan ra'ayin da ya yaɗu ya fi kusa da wauta fiye da hankali.

A mafi yawan lokuta, gaskiya ba ta kasancewa a ɓangaren da mafi yawan mutane suka karkata. Domin ko a cikin Alkur'ani Allah ya yi nuni da cewa, Idan mutum ya bi da yawan mutane da ke rayuwa a doron kasa za su ɓatar da shi daga bin gaskiya. 

Haka nan kuma, mutanen da da na yanzu sun yi tarayya akan cewa, idan wani mutum ya yi fice ko ya shahara a wani fanni na Ilimi ko na rayuwa, mutane na kokarin fassara duk wata mahanga ko fahimtar shi a matsayin daidai da kuma fassara duk wata mahanga da ta saɓa da na shi a matsayin shirme. Kari akan haka, suna  yin kokarin kwaikwayon rayuwar irin wadannan mutanen ba tare da yin la'akari da wace hanya suka bi su ka kai ga wannan matsayin ba. 

Ko kuma su yi nazari akan mahanga ko fahimta da wannan fitaccen mutumin ya yi riƙo da shi ba. Kawai su kan tafi ne kai tsaye su gaskata abin kawai saboda wannan shahararren mutumin. 

Kamar yadda ya ya zo a tarihi cewa, kusan dukkan Annabawa da Allah ya aiko sun yi kokarin kawar da irin wannan tunanin daga ƙwaƙwalen al'ummar su. Domin kusan dukkan al'ummu sai da suka tuhumi Annabawa da cewa suna so su kawar da su daga kan hanyar da manyan su (Kakanni da fitattun mutanen cikin su) ke kai. 

Kuma har a yau ɗin nan idan mutum ya yi ƙoƙarin bayyana wata fahimtar shi da ta saɓa da fahimtar irin wadannan mutanen, da yawan mutane ba za su yarda da shi ba. Wasu cewa ma za su yi ya yi hakan ne kawai saboda shi ma ya shahara kamar yadda Larabawa ke cewa "ka saɓa (da fahimtar da yawa daga cikin mutane) za a san ka" 

A hakikanin gaskiya, ita gaskiya ba ta bukatar amincewar mutane (shahararru da wanda ba su shahara ba) domin ta zama gaskiya. Haka nan kuma saboda mafi rinjayen mutane sun ƙaryata gaskiya ba zai sa ta tashi a matsayin ta na gaskiya ba. 

Sau da yawa mutane na ƙoƙarin bayyana saɓanin gaskiya a matsayin gaskiya ne saboda guje wa takalifin da ita gaskiyar ke zuwa da shi ko kuma kaucewa saɓa wa da mafi yawancin mutane. Domin da yawan mutane sun fi so ana damawa da su cikin al'umma.

No comments