Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi
lale marhabin da matakin gwamnatin Amurka na cire kasar daga sahun wadanda take
yi wa kallon masu tauye ‘yancin yin addini.
A cikin wata sanarwa da ya fitar,
Ministan YaÉ—a labarai da al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed ya kira
matakin na Amurka da adalci.
Rahotanni sun nuna cewa a jiya ne
Amurkar ta cire sunan kasar daga jerin ƙasashen da take zargi da tauye yancin
addini kwana É—aya kafin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya isa Nijeriyar
a yau Alhamis.
0 Comments