Daga Muhammadu Haruna Mazauna garin zazzaga da makwabtansu na karamar hukumar Munya a jihar Neja sun tsere daga gidajensu a jiya...
Daga Muhammadu Haruna
Mazauna garin zazzaga da makwabtansu na karamar hukumar Munya a jihar Neja sun tsere daga gidajensu a jiya Asabar a yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko haram ne suka sabunta hare-hare a kan kauyukan yankin tare da yin awon gaba da dimbim jama'a kamar yadda RFI ta labarto.
Wannan al’amari ya zo ne ‘yan kwanaki bayan sace mutum 30 a garin na Zazzaga.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan ta’addan na cin karensu ba babbaka, kuma halin da ake ciki babu kowa a garin.
Rahotanni sun ce a kauyen Kachiwe, ‘yan sa kai sun tunkari ‘yan ta’addan bayan da suka sace mutane da ba a tantance adadinsu ba, kuma a yayin artabun ne wasu da dama suka kubuta.
Jaridar ‘Daily Trust’ ta ruwaito wata majiya na cewa a tsakanin Juma’a da Asabar ‘yan ta’adan yi awon gaba da mutane da dama, kuma yanzu haka masu barin kauyukan sun rasa inda za su sa kansu.
No comments