Daga Abubakar Musa Zariya Tun ranar 17 ga watan Nuwamban 2021, 'Dan majalisar Tarayya mai wakiltar Sabon Gari, Honorabul Gar...
Daga Abubakar Musa Zariya
Tun ranar 17 ga watan Nuwamban 2021, 'Dan majalisar Tarayya mai wakiltar Sabon Gari, Honorabul Garba Datti Muhammad ya shirya burge mata da matasa kimanin dari uku (300) ta hanyar koya musu sana'o'i daban-daban domin dogaro da kansu.
Tuni shirin ya gudana a wurare daban-daban wanda ya hada da;
1) TEEJAY PALACE HOTEL:
Ana koyar da sana'ar gyaran gashi (Hair dressing).
2) DOVE EVENTS CENTER (KWANGILA):
Ana koyar da sana'o'in noma nau'i daban-daban (farming).
3) RECREATION CLUB (TOWNSHIP STADIUM): Ana koyar da yadda ake hada sabulun wanka dana wanki da sauran su.
Wannan koyarwa an dauki kwanaki uku cur ana antayawa jama'ar ilmomi nau'i daban-daban domin kawo ci gaban karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya.
Wakilinmu ya shaida yadda tarukan suka gudana. Bayan an kammala bayar da horon take aka ba su takardar shaidar kammala karatun.
Alhaji Ado Samaru shi ya wakilci dan majalisa a wajen taron a jawabinsa yayin kammala taro ya mika godiya ne ga mai gidan na sa Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo bisa kokarin da yake yi a fadin karamar hukumar ta Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya.
Ado ya ce ba a taba samun dan majalisa mai kishin mutanensa ba kamar Garba Datti Muhammad Babawo ba. Ya ce shiyasa ake ce masa (Dambu Mai Hawa Uku).
Karshe ya mika sakon mai girma dan majalisar ga mahalarta taro ta inda ya tabbatar da cewa wannan horon da suka samu gami da tallafi ba an gama bane somin tabi ne.
Kuma ya yi kira ga wanda suka sami tallafin da su yi amfani da abin da suka samu a hanyar da ta dace.
Hajiya Lauran na daya daga cikin wadanda suka sami damar samun wannan horo a yayin da ta ke zantawa da manema labarai bayan ta karbi takardar shaidar halartar horon sai ta ce; gaskiya ta ji dadin kasantuwarta a cikin wanda suka sami horo a wannan lokaci kuma ta sha alwashin za su yi kokari wajen yin amfani da abin da suka samu a inda ya dace.
Karshe ta yi godiya ga shi dan majalisar kuma ta yi fatan Allah ya biya masa bukatarsa duniya da lahira.
Tuni jama'a ke fatan alheri yayin da wannan tagomashin ke isa cikin mazabun dake karamar hukumar ta Sabon Gari.
No comments