Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum uku da kuma ceto mutum shida sakamakon rushewar wani gini a jihar Legas da ke kudu maso yammacin N...
Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum uku da kuma ceto mutum shida sakamakon rushewar wani gini a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
A yau Litinin da rana ne ginin mai hawa 25 wanda ake kan aikin gininsa ya rushe inda lamarin ya rutsa da mutane da dama.
Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu sun shaida wa BBC cewa mutane da dama ne ke cikin ginin da suka haÉ—a da ma'aikata da Æ´an kwangila a lokacin da abin ya faru.
Zuwa yanzu an yi amannar kusan mutum 100 ne lamarin ya rutsa da su.
Tuni aka kai kayayyakin aikin ceto wajen da na gano ko akwai masu rai a ƙarƙashin ɓaraguzan.
No comments