Tsohon dan wasan Super Eagles, Garba Lawal ya ce, a yanzu damuwarsa ba ta ta’allaka ba kan wanda zai zama sabon kocin Najeriya, amma ta ya...
Tsohon dan wasan Super Eagles, Garba Lawal ya ce, a yanzu damuwarsa ba ta ta’allaka ba kan wanda zai zama sabon kocin Najeriya, amma ta yaya ne kasar za ta samu gurbin halartar gasar cin kofin duniya a Qatar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka zafafa kiraye-kirayen hukumar kwallon kafar kasar ta NFF da ta gaggauta sallamar kocin super Eagles Gernot Rohr, wanda ake ganin ya rasa tabuka abin kirki.
Kodayake wasu majiyoyin bayan fage masu tushe daga hukumar ta NFF sun ce, nan kusa za a kori kocin mai ruwa biyu, wato daga Faransa da Jamus.
A halin yanzu anan kan tattara takardun sallamar sa a cewar rahotanni na bayan fagen.
Tuni wasu daga cikin ‘yan Najeriya suka fara bada shawarar daukar Emmanuel Amunike tare da Salisu Yusuf don jagorantar tawagar ta Super Eagles.
Sai dai a cewar Garba Lawan, zancen nada koci ba shi ba ne ya dame shi, amma ta yaya Najeriyar za ta samu tikitin zuwa Qatar.
a cewarsa, koda Najeriya ta dauko Jose Mourinho a yanzu, amma ta rasa damar samun tikitin, hakan shirme ne.
No comments