Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Na Fara Waka Ne Saboda Kaunar Da Nake Yi Wa Naziru Sarkin Waka, Inji Mawaki SA-Yarima

Mubarak (SA-YARIMA) matashin da ya fara waka saboda kaunar Naziru Sarkin waka, hakan ya sanya ya fara wakensa na farko da yi wa ...


Mubarak (SA-YARIMA) matashin da ya fara waka saboda kaunar Naziru Sarkin waka, hakan ya sanya ya fara wakensa na farko da yi wa Naziru cikin harshen Fulatanci, Hausa da Larabci da kuma Turanci.

Matashi mai suna Mubarak wanda ya fito daga garin Bauchi a Arewacin Nijeriya; ya wake Naziru Sarkin waka cikin harshen Hausa da Fulatanci, Turanci, Larabci a salon waka sama da biyar.


Matashin ya bayyanawa Jaridar Inuwar Labarai cewa, ya fara waka saboda kaunar Naziru Sarkin waka shi yasa ya fara wake shi.

Kasancewar matashin a da'irar waka ta ba shi daman sauya tunanin cewa a kasar Hausa yana iya rera waka da Harshen Hausa sannan ya kuma rera da harshen Fulatanci, gami da turanci da kuma larabci a lokaci guda cikin qafiya tare da kiyaye harshen waqa.

Matashin wanda tauraruwarsa ta fara haskawa ya fito ne daga jihar Bauchi in da yake amsa laqabin S-A YAREEMA a fagen  waqa.

Zaqaqurin Matashin Mawaqin da yana zuwa sabon wakokin da yake nishadantar da masu sauraronsa.

Matashin ya ci gaba da bayyana mana cewa: "Kasantuwar waqa ta zama wata hanya ta isar da saqo cikin al'umma kuma tana daga cikin hanyoyin da suke da tasiri mai qarfi."In ji shi.

Matashin ya kasance wanda yake iya rera waka cikin Harsunan Hausa da Fulatanci da turanci da kuma Larabci, mawakin ya bayyana mana cikin harsunan guda hudu ba da harshen da bai wake gwanin na sa ba.

Domin Neman mawakin za a iya samunsa a wannan lamba kamar haka "0813 581 5527". 

Sannan za a iya samun wakokinsa a Youtube na "Inuwar Labarai TV"

No comments