Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Pantami Ya Cancanci Zama Farfesa -Martanin FFK Ga ASUU

Tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama, Femi Fani-Kayode, ya soki Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa, ASUU a kan ta kafa kwa...


Tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama, Femi Fani-Kayode, ya soki Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa, ASUU a kan ta kafa kwamitin bincike kan bai wa Ministan Sadarwa, Isah Pantami muƙamin Farfesa a fannin tsaro ta yanar gizo.

A saƙonnin da ya riƙa wallafawa a shafinsa na Twitter, Fani-Kayode, wanda kwanan nan ya sauya sheƙa zuwa APC, ya ce Pantami ya cancanci a bashi muƙamin Farfesa.

"Wanne laifi Pantami ya yi wa ASUU ne? Yaushe za su daina wannan tsanar ne? Na san Pantami sosai kuma ya cancanci ya zama Farfesa. Ya kamata mu riƙa nunawa junan mu so da ƙauna ba ƙiyayya, tsana, ƙage da ƙarya da kuma nuna bambancin addini ba.

A watan Satumba ne dai Jami'ar Fasaha ta Tarayya ta Owerri, FUTO ta sanar da bai wa Pantami lambar girma ta Farfesa, sannan ASUU, reshen jami'ar ta tabbatar da shi.

Amma uwar ƙungiyar ASUU ta ƙasa ta ce ba da yawun ta a ka ba shi Farfesan ba kuma ta kafa kwamiti don binciken sahihancin naɗin na shi.

No comments