BBC ta labartocewa an bayyana Pedri na Barcelona a matakin gwarzon matashin dan kwallon kafa na Turai na bana da Tuttsports za ta karrama...
BBC ta labartocewa an bayyana Pedri na Barcelona a matakin gwarzon matashin dan kwallon kafa
na Turai na bana da Tuttsports za ta karrama a kyauta ta 19 jumulla.
Jaridar ta Italiya ta bayyana
matashin dan wasan mai shekara 18 a matakin babu kamarsa a fagen taka leda a
tsakanin masu shekara kasa da shekara 21 da haihuwa a kyautar da ake kira
Golden Boy award.
'Yan jarida 40 suka kada kuri'ar don
fitar da zakaran bana, inda 26 suka zabi Pedri da tara daga ciki da suka zabe
shi a mataki na biyu, sannan uku daga ciki suka sa dan wasan Barcelona a matki
na uku.
Hakan na nufin Pedri ya hada maki
318 kenan, inda Jude Bellingham ya yi na biyu da maki 119, kuma ba a taba samun
tazara mai yawa tsakanin na daya da na biyu ba sai a wannan karon a tarihin
kyautar.
Matashin ya buga wa tawagar Sifaniya
karawa 73 har da Euro 2020 da gasar Olympic da aka yi a Tokyo da tawagar ta
samu azurfa.
Lionel Messi ne ya fa lashe kyautar
da aka fara a karon farko a 2005, inda Cesc Fabregas ya zama gwarzo a 2006,
sannan Kun Aguero ya zama zakara a 2007 a cikin wadanda suke daga Barcelona.
Haka kuma Pedro Gonzalez ya ci
kyautar da Erling Haland ya lashe a bara.
No comments