Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Rashin Man Fetur Zai Tsananta A Yayin Da NUPENG Ta Shirya Tafiya Yajin Aiki

Ƙungiyar Ma’aikatan Fetur da Gas (NUPENG) ta yi barazanar fara yajin aiki. Hakan alama ce mai nuna cewa nan da kwanaki kaɗan wah...


Ƙungiyar Ma’aikatan Fetur da Gas (NUPENG) ta yi barazanar fara yajin aiki. Hakan alama ce mai nuna cewa nan da kwanaki kaɗan wahalar fetur da gas za dawo kenan a faɗin ƙasar nan kamar yadda Premium Times ta labarto.

Sanarwar barazanar fara yajin aikin na cikin wata takardar da shugabannin NUPENG suka fitar, bayan tashi daga taron da suka yi a ranar Litinin.

Shugaban ƙungiya Williams Akhoreha da sakataren ƙungiya Olawale Afolabi ne su ka sanya wa takardar bayan taron hannu.

Ƙungiyar ta ce ta fitar da sanarwar za ta tsunduma yajin aiki ne tun a yarjejeniyar da aka cimma ta taron wakilan ƙungiyar na ƙasa a ranar Alhamis.

NUPENG ta bayyana cewa ma’aikatan ƙungiyar akwai ɗimbin masu yawa daga cikin su, waɗanda ba biya albashin su da alawus na tsawon lokaci ba. Kuma hakan na ɗaya daga cikin dalilan tafiyar da za su yi yajin aiki.

Sannan kuma NUPENG ta yi ƙoƙarin cewa akwai ɗimbin kuɗaɗen sallamar da aka ƙi biyan wasu mambobin NUPENG da dama, waɗanda kamfanin mai na Chevron ya sallama daga aiki, tun cikin shekarar 2012.

NUPENG ta zargi sallamar ma’aikatan Chevron daga aiki, don kawai sun shiga cikin ƙungiyar NUPENG, a matsayin su na ma’aikatan wucin-gadi.

Sau da NUPENG ta ce wasu daga cikin su fa sun kai shekaru 10 su na aiki, wasu ma sun shafe shekaru sama da ashirin.

NUPENG ta ce haka aka sallame su ba tare da an biya su haƙƙoƙin su ba.

“Saboda haka NUPENG ta na sanar da Ma’aikatar Ƙwadago cewa ta bada wa’adin kwanaki 14 domin a biya mu haƙƙoƙin mu, ko kuma mu tafi yajin aiki. Wannan gargaɗi zai fara aiki tun daga ranar 15 Ga Nuwamba, 2021.”

“Akwai kuma matsalar ma’aikatan PYRAMIDT, waɗanda aka kwashe shekaru da dama a na yin ƙwallo da su. Idan an tura su ga wannan ƙungiya, gobe kuma sai a tura su ga wata.

“Akwai kuma matsalar ma’aikatan haƙo mai na Rijiyar Mai Lamba 42, wadda mallakin NPDC ne. Har yau ba a biya su albashi ba, tsawon watanni 10.

“Kamfanin Agip Oil ya na amfani da dalilin cutar korona, ya tura ma’aikatan sa zaman gida tun 2020, a gefe ɗaya kuma ya na ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi Agip ɗin na biyan su ladar aikin su a kowace rana.

No comments