Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Rikicin Cikin Gidan APC Na Kara Kamari A Zamfara

Al'amurra na ci gaba da zafafa tsakanin bangarorin jamiyyar APC na jihar Zamfara akan batun zaben sabbin shugabannin jamiyya...


Al'amurra na ci gaba da zafafa tsakanin bangarorin jamiyyar APC na jihar Zamfara akan batun zaben sabbin shugabannin jamiyyar a matakai daban daban na jihar, a yayin da bangaren Sanata Kabiru Marafa ke ci gaba da gudanar da zaben shugabannin a karkashin kulawar bangaren tsohon gwamna Abdulaziz Yari.

Dama dai shugaban riÆ™o na APC a jihar Zamfara da ke a bangaren Abdulaziz Yari Lawal M Liman ya shaida wa magoya bayansu cewar su nisanci taron zaben (Congress) da bangaren gwamna Bello Matawalle suka  bayyana shi a matsayin taron da bashi akan doka. .   

A wannan Asabar ma taron na zaben shugabannin kananan hukumomi a jihar ta Zamfara ya rabu gida biyu  yayin da bangaren gwamna Matawalle a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Nasiha sun gudanar da nasu taro yayin da bangaren Kabiru Marafa suma ke nasu duk a wuni guda. . 

A wata rubutacciyar sanarwa da bangaren tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya fitar wannan Assabar dauke da sa hannun Ibrahim Dan Madamin Birnin Magaji, bangaren na tsohon gwamna na cewar sun bukaci magoya bayansu su zura ido ne kawai suna masu dogaro da cewar yanzu haka akwai shara'a a gaban babbar Kotun tarayya dake nan Gusau kan wannan taro don haka ba za su shiga taron ba har sai Kotu ta gama yanke hukunci akai. .  

A bisa haka inji sanarwar bangaren Abdulaziz Yari ya zabi ya bi ka'ida wajen mutunta umurnin Kotu. Dama dai Alkalin Kotun Justice Aminu Bappa ya dage zaman Kotun har zuwa ranar biyu ga watan Disamba domin yanke hukunci.

To ko me bangaren gwamna Matawalle zasu ce dangane da wannan, tambayar da muka yi wa Gado Sony wani makusancin gwamna Matawalle ta wayar tarho ya kuma ce baida abinda zai ce, a yayin da Hassan Nasiha wanda shine shugaban rikon kwarya na APC a bangaren gwamna Matawalle bai dauki kira ba bai kuma maida sakon kar-ta-kwana na wayar Tarho da muka aika masa ba. 

To sai dai a ta bakin Bello Bakyasuwa mai magana da yawun Sanata Marafa a zantawarmu ta wayar tarho, sun dauki matakin yin nasu taron ne domin nuna wa uwar jamiyyar cewa ba zasu bari wadanda ba cikakken ya'yanta ba, su wargaza mata tsari. Amma a cewar sa, duk da haka su masu ladabi ne ga umurnin kotu, sannan daukar matakin yin taron da suka yi ba yana nufin suna da matsala ne da ubangidansu tsohon gwamna Abdulaziz Yari ba ne. 

-RFI

No comments