Dan wasan Mancester United, Cristiano Ronaldo da na Liverpool, Mohamed Salah suna cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon Fifa na bana ...
Dan wasan Mancester United, Cristiano Ronaldo da na Liverpool, Mohamed Salah suna cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon Fifa na bana don lashe kyautar Fifa Best 2021.
A bangaren mata kuwa da ke takarar wadda tafi fice a taka leda a 2021 har da 'yar wasan Manchester City, Ellen White da takwararta Lucy Bronze.
'Yan kwallon Chelsea, N'Golo Kante da Jorginho suna ciki har da fitatcen dan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne.
Za a yi zaben ne don tantance gwanayen da suka taka rawar gani a tamaula tsakanin 8 ga watan Oktoban 2020 zuwa 6 ga watan Agustan 2021.
Za a bayyana gwarzaye ranar 17 ga watan Janairun 2022, bayan an yi zabe tsakanin koci koci da kyaftin kyaftin din tawagar mambobin Fifa da wasu 'yan jarida.
Ga jerin kyautukan da za a lashe
Macen da ba kamarta a taka leda
Stina Blackstenius (Sweden/BK Hacken)
Aitana Bonmati (Spain/Barcelona)
Lucy Bronze (England/Manchester City)
Magdalena Eriksson (Sweden/Chelsea)
Caroline Graham Hansen (Norway/Barcelona)
Pernille Harder (Denmark/Chelsea)
Jennifer Hermoso (Spain/Barcelona)
Ji So-yun (South Korea/Chelsea)
Sam Kerr (Australia/Chelsea)
Vivianne Miedema (Netherlands/Arsenal)
Ellen White (England/Manchester City)
Alexia Putellas (Spain/Barcelona)
Christine Sinclair (Canada/Portland Thorns)
Dan kwallon da yafi kowa taka rawar gani
Karim Benzema (France/Real Madrid)
Kevin de Bruyne (Belgium/Manchester City)
Cristiano Ronaldo (Portugal/Juventus/Manchester United)
Robert Lewandowski (Poland/Bayern Munich)
Lionel Messi (Argentina/Barcelona/Paris Saint-Germain)
Neymar (Brazil/Paris Saint-Germain)
Erling Braut Haaland (Norway/Borussia Dortmund)
Jorginho (Italy/Chelsea)
N'Golo Kante (France/Chelsea)
Kylian Mbappe (France/Paris Saint-Germain)
Mohamed Salah (Egypt/Liverpool)
Macen da ke horar da tamauala da ba kamarta
Lluis Cortes (Spain/Barcelona)
Peter Gerhardsson (Sweden/Tawagar Sweden)
Emma Hayes (England/Chelsea)
Beverly Priestman (England/Tawagar Canada)
Sarina Wiegman (Tawagar Netherlands da ta Ingila)
Koci namiji da yafi yin fice
Antonio Conte (Italy/Inter Milan/Tottenham Hotspur)
Hansi Flick (Jamus/Bayern Munich/Tawagar Jamus)
Pep Guardiola (Spain/Manchester City)
Roberto Mancini (Italy/Tawagar Italiya)
Lionel Sebastian Scaloni (Argentina/Tawagar Argentina)
Diego Simeone (Argentina/Atletico Madrid)
Thomas Tuchel (Germany/Chelsea)
Macen da ba kamarta a tsare raga
Ann-Katrin Berger (Germany/Chelsea)
Christiane Endler (Chile/Paris Saint-Germain/Lyon)
Stephanie Lynn Marie Labbe (Canada/FC Rosengard/Paris Saint-Germain)
Hedvig Lindahl (Sweden/Atletico Madrid)
Alyssa Naeher (USA/Chicago Red Stars)
Maza masu takarar golan da yafi kwazo
Alisson Becker (Brazil/Liverpool)
Gianluigi Donnarumma (Italy/AC Milan/Paris Saint-Germain)
Edouard Mendy (Senegal/Chelsea)
Manuel Neuer (Germany/Bayern Munich)
Kasper Schmeichel (Denmark/Leicester City)
-BBC
No comments