Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sababbin Jiragen Saman Nijeriya Zai Fara Aiki A Watan Afrilu - Sirika

Daga Wakilinmu Gwamnatin Nijeriya ta ce sabon kamfanin jiragen ta da aka yi wa suna ‘Nigeria Air’ zai fara aiki daga watan Afril...

Daga Wakilinmu

Gwamnatin Nijeriya ta ce sabon kamfanin jiragen ta da aka yi wa suna ‘Nigeria Air’ zai fara aiki daga watan Afrilun shekara mai zuwa bayan dogon tsaikon da aka samu.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya sanar da cewar wani kamfani ne zai kula da hada hadar jiragen, wanda gwamnati za ta zuba jarin kashi 5 a cikinsa, sai kuma wasu ‘yan kasuwar za su zuba kashi 46, yayin da za a sayarwa sauran mutane masu bukatar sanya hannun jari kashi 49 kamar yadda RFI ta labarto.

Hadi ya ce idan kamfanin ya fara aiki zai samar da ayyukan yin ga mutanen da za su kai 70,000.

Nijeriya ta dade tana kokarin kafa kamfanin jiragen sama amma kuma wasu matsalolin cikin gida sun hana ta samun nasara.

A shekarun da suka wuce, gwamnatin Nijeriyar ta gabatar da shirin kafa kamfanin jiragen a wani bikin da aka yi a birnin Landan, amma kuma daga bisani sai aka dakatar da shirin.

A shekarun 1970 Nijeriya ta kafa kamfanin ‘Nigeria Airways’ wanda ya yi fice a nahiyar Afirka amma daga bisani sai ya durkushe, abin da ya sa gwamnati ta sayar da kadarorinsa ta kuma dakatar da shi baki daya.

Kasashen Afirka da dama na da kamfanin jiragen sama mallakar kan su wadanda suke matukar tasiri wajen zirga-zirga a cikin Afirka da kuma kasashen duniya saboda kyakyawan tsarin yadda ake tafiyar da su.

Daga cikin irin wadannan kamfanoni akwai Ethiopian Airline na kasar Habasha da Kenyan Airline na kasar Kenya da Egypt Air mallakar kasar Masar da South African Airline mallakar Afirka ta Kudu da kuma Maroc Air mallakar kasar Morocco.

No comments