Sabon Nau’in Korona Na Omicron Mai Hatsari Ya Dami Duniya


Ministocin lafiya na kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya da ake kira G7 za su yi wani taro domin samar da matsaya kan sabon nau'in cutar korona na Omicron.

An fara gano wannan nau'in cutar ne a Afirka ta Kudu a ranar Laraba da ta gabata kuma ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar.

Kasashen France da Switzerland da Canada duk sun tabbatar da bullar cutar a kasashen nasu a ci gaba da gudanar da binciken kimiyya kan wannan nau'i na annoba na Omicron.

Gwamnatin Najeriya ta ce nau’in cutar bai É“ulla a Æ™asar ba kawo yanzu, kamar yadda hukumar da ke É—akile cutuka masu yaÉ—uwa ta ce ta É—auki matakai na É—akile cutar a Æ™asar kamar yadda BBC ta labarto. 

Post a Comment

0 Comments