Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sabuwar Cutar Korona Ta "Omicron" Ta Ɓulla A Kasar Belgium

Daga Umar Shuaibu A yayin da Hukumomin Turai ke bayyana damuwar su dangane da yaɗuwar sabuwar nau'in cutar Korona da aka sa ...


Daga Umar Shuaibu

A yayin da Hukumomin Turai ke bayyana damuwar su dangane da yaɗuwar sabuwar nau'in cutar Korona da aka sa wa suna Omicron a yankin da kuma daukan matakan gaggawa domin dakile faruwan hakan, kasar Belgium ta sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar. 

Wannan nau'in na cutar ya fara ɓulla ne a Kasar Afrika ta Kudu. Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana bayyana ciwon a matsayin abun damuwa sosai duba da yadda wannan ciwon ya ke yaɗuwa cikin sauki. Hukumar ta kuma kara da cewa tana kara nazarin ciwon da kuma hanyoyin da za a bi wurin dakile yaduwar ta. 

Kasar Belgium ta zama ƙasa ta farko a Nahiyar Turai da ta sanar da samun wanda ya kamu da "Omicron". Ministan Lafiyan kasar ya bayyana cewa wata mata ce da ba ta karbi riga-kafi ba ke dauke da cutar. Bincike ya nuna cewa, matar ta dawo daga ƙasar Misra a ranar 11 ga watan Nuwamba ta kuma fara nuna alamomin ciwon a ranar 22 ga watan Nuwamba.

A lokaci guda kuma, kamfanin magunguna na Biontec ya bayyana cewar yana bincike domin gano riga-kafin da zai iya yin tasiri a kan Omicron.

No comments