Gwamnatin Birtaniya ta ce daga yanzu duk wani bako da ya ziyarci kasar zai killace kan sa har sai ya gabatar da shaidar dake nun...
Gwamnatin Birtaniya ta ce daga yanzu duk wani bako da ya ziyarci kasar zai killace kan sa har sai ya gabatar da shaidar dake nuna cewar baya dauke da cutar korona, sakamakon samun sabon nau’in cutar da ake kira Omicron.
Firaministan kasar Boris Johnson ya bayyana haka ga manema labarai, sa’oi bayan an gano mutane biyu na dauke da sabon nau’in cutar wadda aka ce ta samo asali daga Afirka ta Kudu.
Tuni kasashen duniya da dama suka sanar da daukar matakan da suka hada da hana bakin da suka fito daga yankin kudancin Afirka shiga cikin su.
(RFI)
No comments