Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Antony Blinken, Sakataren gwamnatin Amurka a fadar gwamnatin Nijeriya ta Villa dake Abuja. Babban ...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Antony Blinken, Sakataren gwamnatin Amurka a fadar gwamnatin Nijeriya ta Villa dake Abuja.
Babban Jami’in Amurkan ya isa fadar gwamnatin Nijeriya ne da misalin karfe 3:47 na yamma a yau Alhamis inda ya gana da shugaban kasar.
Bayan ganawarsa da Buhari, ana sa ran zai kuma gana da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo inda ake tsammanin sanya hannun yarjejeniya a tsakanin kasashen biyu.
Blinken zai gabatar da taron manema labarai, inda a tare da shi ministan harkokin wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama, zai kasance tare da shi kafin barin fadar gwamnatin.
Wasu daga cikin hotunan ganawar;
No comments