Daga Zubairu Lawal Mista Mazou ya nuna damuwarsa kan yadda al'ummar jihar Borno ke yaduwa a wurare daban daban ciki harda k...
Daga Zubairu Lawal
Mista Mazou ya nuna damuwarsa kan yadda al'ummar jihar Borno ke yaduwa a wurare daban daban ciki harda kasashen ketare.
Ya ce sama da mutum 67, 000 ya jihar Borno ke gudun Hijira a kasar Kamaru, wannan abin a duba rayuwarsu ne.
Mista Mazou ya jinjinawa Gwamnatin jihar Borno kan yadda take bada kulawa ga al'ummar dake rayuwa a sansanin 'yan gudun Hijirar.
Ya ce; sanin kowanne mutanen dake rayuwa a ire-iren wadannan wuraren suna da bukatar kulawa masamman a fannin ci da sha da kuma bangaren kiwon lafiya.
Ya ce; mutanen dake rayuwa a sansanonin gudun Hijira mutane ne da rayuwarsu take da muhimmanci da ba kawai sun sanya kansu ne na zama a nan bane, lalurace wanda kuma dole ya sanyasu suke rayuwa a wanan wurin.
Mista Mazou ya ce; kulawar da Gwamnati take bai wa 'yan gudun Hijirar a fannin kiwon lafiya da al'amuran yau da kullum babban abin a yaba ne.
Ya ce; a kokarin gwamnatin na maida 'yan gudun Hijira zuwa garuruwansu, aiki ne na ci gaba amma ba za a kammala shi a kankanin lokaci ba.
Ya Kuma yabawa kungiyoyin dake bada gudumawa a sansanonin gudun Hijira dake yankunan da sauransu.
No comments