Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Saraki Ya halarci Ɗaurin Auren Ɗiyar Sheikh Bala Lau

A yau Juma'a ne tsohon Shugaban majalisar dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya...


A yau Juma'a ne tsohon Shugaban majalisar dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya halarci ɗaurin auren diyar shugaban kungiyar Izala ta Nijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Auren wanda aka ɗaura a babban masallacin Juma'a na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake unguwar Malali a Jihar Kaduna ya samu halartar manyan mutane da malamai daga sassan Nijeriya.


Wazirin na Ilorin ya shaidi auren wanda aka kulla tsakanin amarya Rufaida Bala Lau da angonta Tijjani Abdullahi Gabba. 

A wani saƙon taya murna da ya ɗora a shafinsa na Facebook, Dakta Saraki ya yi wa ma'auratan fatan alheri tare da addu'ar Allah Ya albarkaci aurensu.

No comments